Fitacciyar ‘yar wasan biathlon ta ƙasar Jamus kuma zakarar zinare a Olympics, Laura Dahlmeier, ta rasu bayan faɗuwa daga wani dutse a arewacin Pakistan yayin da take hawa Laila Peak da ke tsaunin Karakoram, inji mai magana da yawun gwamnatin Gilgit-Baltistan, Faizullah Faraƙ, ranar Laraba.
An bayyana cewa, ƙoƙarin ceto Dahlmeier ya ci tura saboda tsananin hadari da ya hana masu ceto isa wurin. Abokin tserenta, Marina Eva, ta tsira daga haɗarin bayan ta turo da siginar neman agaji a ranar Litinin, wanda hakan ya tayar da tawagar ceto. A ƙarshe dai an tabbatar da mutuwar Laura ranar Laraba, amma ba a iya ɗauko gawarta ba saboda yanayin ƙasa da iska.
A cewar wata sanarwa da aka wallafa a shafin Instagram na Laura, marigayiyar ta bayyana a cikin wasiyyarta cewa a lokacin da wani hatsari ya faru da ita, ba za ta so a sanya rayuwar wani cikin haɗari don ceto ko ɗauko gawarta ba. Wannan ya sa hukumomi ke jiran amincewar iyalanta kafin ɗaukar mataki na gaba.
Shugaban Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya bayyana alhini bisa rasuwar Laura, yana cewa, “Laura Dahlmeier ta kasance jakadiyar Jamus a duniya, kuma abin koyi ce wajen nuna zaman lafiya da mutuntaka tsakanin ƙasashe.” Ya ƙara da cewa, bayan nasarar ta na Olympics a 2018, ya karrama ta da lambar yabo mafi girma a wasannin Jamus, wato Silver Laurel Leaf.
A cewar ƙungiyoyin tafiye-tafiye, marigayiyar ta sami raunika a matsayi mai tsayi na mita 5,700 (kimanin kafa 18,700) da rana ranar Litinin. A cewar tawagarta, abokiyar tafiyarta ta yi ƙoƙarin taimaka mata na tsawon sa’o’i amma kasa yi saboda tsananin haɗari.
A ƙarshe, iyalan Laura sun gode wa duk waɗanda suka ba da taimako a ƙoƙarin ceto ta, tare da roƙon a mutunta wasiyyarta.
