Kwararru na kokawa kan taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Kwararru kan harkar tsaro a Nijeriya na ci gaba da nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a ƙasar nan. Shugaban kamfanin Priɓate Guard Security Company da ke Kano, Dr. Idris Adamu Pukuma, ya bayyana hakan a saƙonsa na taya ’yan Nijeriya murnar shigowar sabuwar shekara.

Dr. Idris, wanda mamba ne a hukumar zartarwa ta ƙungiyar jami’an tsaro masu zaman kansu ta ƙasa, ya ce sace ɗalibai daga makarantu ya zama abin takaici kuma barazana ga martabar ƙasa a idon duniya.

Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kano, inda ya ce duk da Nijeriya na da ƙwararrun jami’an tsaro, halin da ake ciki na nuna buƙatar ƙarin tsari da haɗin kai.

Ya nuna goyon bayansa ga shirin kafa ’yan sandan jihohi, amma ya ja hankalin gwamnoni da kada a mayar da su kayan siyasa. Ya kuma buƙaci gwamnati ta riƙa amfani da hukumomin tsaro masu zaman kansu saboda ƙwarewarsu da rawar da suke takawa wajen rage rashin aikin yi.

Dr. Idris ya yi kira ga iyaye da shugabannin makarantu da su ƙara sanya ido kan zirga-zirgar yara, musamman a makarantu, domin gujewa faɗawa hannun masu aikata laifi.

By ukarofi