Yadda taron Muryar Birnin Kudu karo na bakwai ya gudana

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

An gudanar da taron shekara-shekara na ƙungiyar Muryar Birnin Kudu karo na bakwai a Makarantar Koyon Aikin Jinya da ke Unguwar Zoma, Birnin Kudu a Jihar Jigawa, wanda ake gudanarwa duk ranar ɗaya ga watan Janairu.

Taron ya haɗa ’ya’yan Birnin Kudu daga sassa daban-daban na ƙasa, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi haɗin kai, ci gaban al’umma da matsalolin yankin. An bayyana cewa Birnin Kudu Allah ya albarkace shi da manyan mutane, ƙasar noma, ma’adanai da albarkatun ruwa.

Shugaban taron, Barista Ali Sa’adu Birnin Kudu, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, ya ce taron na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa zumunci da tattauna hanyoyin ci gaban gari. Ya yi kira ga matasa da su rungumi ilimi da sana’o’i domin dogaro da kai.

Shugaban ƙungiyar Muryar Birnin Kudu, Alhaji Ahmad Sa’id Kangire, ya bayyana nasarorin da ƙungiyar ta samu cikin shekara bakwai, ciki har da gabatar da kundin buƙatun al’umma ga Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi Danmodi.

Ya ce kundin ya ƙunshi buƙatu a fannoni kamar ilimi, noma, tituna, ruwa, kiwon lafiya, tsaro da kasuwanci, inda tuni aka fara ɗaukar wasu daga cikinsu a jerin ayyukan gwamnati.

Kangire ya ce duk da nasarorin da aka samu, ƙungiyar na fuskantar ƙalubale da suka haɗa da ƙarancin kuɗi da nauyin aiki, amma za su ci gaba da bibiyar ayyukan da aka nema domin amfanin al’umma.

A ƙarshe, ya yaba da gudunmawar masarautar Dutse, malamai, ’yan kasuwa, ’yan siyasa da dukkan masu ruwa da tsaki, tare da fatan alheri ga mahalarta taron.

By ukarofi