Kwastom za ta ɗauki sabbin ma’aikata 3,927

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kwastom ta Nijeriya ta amince da ɗaukar ma’aikata 3,927 tare da ba da ƙarin girma na musamman ga ma’aikatan da suka kware domin magance giɓin ma’aikata da inganta harkokin hukumar.

An yanke wannan shawarar ne biyo bayan sake duba ayyukan hukumar ta NCS a shekarar 2024, wanda ya nuna nasarar da hukumar ta samu wajen daƙile fasa-kwauri da bunƙasa kasuwanci mai matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi.

Hukumar ta yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa gagarumin rawar da take takawa wajen haɓaka farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya, musamman ganin yadda gwamnatin ta tsara kashe Naira tiriliyan 48 a shekarar 2025.

A yayin taron kwamitin karo na 61 da aka gudanar a ranar Laraba, 18 ga watan Disamba, a hedikwatar kwastam da ke Maitama, Abuja, Ministan Kuɗi Olawale Edun ya jaddada muhimmancin hukumar ta NCS.

Taron ya biyo bayan gabatar da kasafin kuɗin 2025 na Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga majalisar dokokin ƙasar.

Wannan kasafin kuɗin yana aiwatar da kuɗaɗen shiga na tiriliyan 35, inda da Kwastom ta taka muhimmiyar rawa.

Minista Edun ya bayyana cewa hukumar ta samar da sama da tiriliyan 5 a watan Nuwamba 2024.

“Hukumar NCS da sauran hukumomi sun taka rawar gani wajen tara kuɗaɗen shiga,” inji shi, yana mai danganta wannan nasarar ga sauye-sauyen Shugaba Tinubu.

Ministan ya ci gaba da bayanin cewa gwamnati na shirin samar da rancen rangwame, tallafin raya ƙasa don samar da sauran naira tiriliyan 13.

Edun ya kammala da yin kira ga jami’an kwastom da su ci gaba da sadaukar da kai ga manufofin ƙasa, yana mai jaddada muhimmiyar rawar da hukumar ke takawa wajen rage fatara da bunƙasar tattalin arziki.

By ukarofi