Babu adalci a mulkin da ake yi a Nijeriya – Dakta Bello

Daga BUSHIRA AMINU NAKURA 

Dakta Ahmad S. Bello malami ne da yake koyarwa a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya. A tattaunawarsa da Blueprint Manhaja a lokacin da yake bayyana irin halin ƙunci da tsadar rayuwa da rashin tabbacin rayuwa da talakan Nijeriya ke fuskanta, saboda taɓarɓarewar harkar tsaro da ilimi ya bayyana rashin mulki na adalci a matsayin silar taɓarɓarewar al’amura a ƙasar da kuma rashin sauraron al’umma da gwamnati ba ta yi balle ta ji damuwarsu. Ya ƙara da  cewa, idan ma ta ji ɗin, ba ta kulawa. saboda ra’ayinta da dukkan abin da ta ga dama ta ke yi, ba wai me al’umma suke so ba. Ga cikakkiyar hirar tasa da ya yi da Wakiliyar Blueprint Manhaja, BUSHIRA AMINU NAKURA. 

MANHAJA: Mene ne cikakken suna da taƙaitaccen tarihinka?

DR. AHMAD: Sunana Dr. Ahmad S.Bello, an haife ni a ƙaramar Hukumar Wudil dake Jahar Kano 11/12/1973. Na yi karatun firamare a ‘Wudil Centre Primary School a shekarar 1979 zuwa 1984. Daga nan na shiga ‘Wudil Teachers College’ (WTC) daga shekarar 1984 zuwa 1988, daga nan  na pleasemen eɗaminetion na tafi zuwa ‘Goɓernment Arabic School Hadejia’ har zuwa 1990 na kammala. Da na gama na wuce cas school wato IJMB kenan wato share fagen shiga jami’a a 1990 zuwa 1991, daga nan ne na samu shiga jami’ar Bayero ta Kano (BAYERO UNIVERSITY KANO) kuma  na shiga levile 2  na kammala a 1995, na karanci Mass cominication Hausa language combine onos, da can ana yin wannan comebination ɗin daga baya ne aka zo aka daina. Bayan nan na je na yi NYC a Jahar Ogun bayan na kammala NYC da yake ina koyarwa ne a FCE ta ogun ɗin sai suka ba ni aiki na fara lacturing a can, daga nan har na kai matakin na zama malami na uku wato ‘Lacturer 3’ ke nan. To haka dai kuma har na zo na yi masters ɗina. Daga Nan har na dawo FCE Zaria. To a FCE Zaria ne cikin nufin Allah har na kai matsayin Chief Lecturer, har na je na yi PHD ɗina a jamiar Ahmadu Bello dake Zariya a  kan harkar adabin fina-finan Hausa, a nan ɓangaren na ƙware, amman na kan kalli abubuwan dake alaƙa da al’adu da waƙe-waƙe da wasannin kwaikwayo da kuma rubutun zube, wannan shi ne tarihina a taƙaice. Ina da mata da kuma yara kuma yanzu haka ni ina zaune a Zaria ne na zama ɗan Zaria wato Bakanon Bazazzagi ne ni.

Ko za ka iya faɗa mana Irin gwagwarmayar rayuwar da ka sha?

Eh to gaskiya ni kam babu wata gwagwarmayar rayuwa da na sha, tunda ni dai na taso cikin gata da kulawar iyayena na taso, kuma na girma da su, sai dai ala kulli halin ita rayuwa ko yaushe takan zo wa mutum da sauyi, wato bayan na tafi Hadejia ba uwa ba uba, babana malamin makaranta ne don garin kwaki muke sha, sannan in je in yi noma in yi barema a ba ni Naira ɗaya da kwabo biyar, ko a ba mu sulai mu uku, mu uku za mu raba silai da sisi. Idan yunwa ta ishe ka, kuma sannan a ƙasa muke takawa zuwa cikin garin Hadejia, mu je mu dawo ba mota a lokacin. To na yi ƙungiyoyi irin na club club da ake yi irin na makaranta, to a nan na ƙara samun juriya na rayuwa sannan bayan da na tafi NYC nan ma babu uwa babu uba, ga shi ban san kowa  ba, gaskiya na ɗan sha wahala kafin in samu mahallin ma da zan zauna, nakan kwana wani lokaci gidan aboki. To wannan shi ne. Amma bayan haka ban samu wani gwagwarmayar rayuwa ba dan kin ga ma ina gama NYC na na samu aiki Alhamdulillah.

Ko akwai wata sana’ar da kake yi bayan aikin gwamnati?

To bayan aikin gwamnati ba ni da wata sana’a da ta wuce noma da kiwo duk da dai noma da kiwo da nake yi ba wani na a zo a gani ba ne face na harkar tsaro, domin kaucewa yunwa saboda muna cikin wani yanayi yanzu a ƙasar nan, yunwa ta yi ma al’umma katutu ta na neman mamaye ko’ina saboda haka ina ɗan yin kiwon kaji ne da kifi, shi ma ɗin a bayan gidana nake yi. Kifi ne ‘yan ƙwaya ɗari biyar zuwa ɗari shida, sai ‘yan kajina kwaya talatin arba’in hamsin domin dai a samu abinci. Wannan shi ne don yanzu ma abincin kajin ya yi tsada sosai, ina ga mun ɗan haƙura da kiwon kajin dan abinda ya rage min bai fi kwayoyi ba, wanda za mu yanka mu cinye abinmu. Amma dai  shi kifi yana nan muna cigaba da yi. Muna ta koyo daga bara dai zuwa bana na yi kiwon kifi sosai wani na ci riba wani na faɗi, dama kuma haka sana’a ta gada kin san dole sai an yi hakuri shi dama kullum mai nema yana cikin abu biyu ne ko uku ko yaci riba ko kuma ya fadi ko kuma yai kan-kan-kan wato shi bai fadi ba kuma bai samu  riba ba. Amma dai ya mayar da kuɗinsa  haka shi ma kuma noman ana yi don ci ne ba wai siyarwa ake ba, domin dai ba ya wuce ‘yan buhu sha biyar ba zuwa ashirin talatin, haka dai shi ma ana yi ne dan tsaro ne, idan wani abun ya taso ana buƙata a ɗauka a siyar a biya buƙata. So bayan nan ina ganin babu wani abu.

Ta wacce hanya kake iya taimaka wa al’umma da wannan aikin naka?

Yara sukan zo mana da ƙorafe-ƙorafe na biyan kuɗin makaranta muna taimaka musu tunda mu daman ilimin shi ne muka maida shi sana’ar mu ita muka sani ita muka iya. Bayan nan akwai masu neman addimition a college. Sukan zo ‘yan unguwa muna taimaka musu har wayau kuma wasu za ki ga cewar ba za su iya biyan kuɗin makarantar ba to su ma mukan ɗan taimaka musu da ko rabi ne sai ana cirewa a albashinmu, to shi ma muna yi ta wannan gefen. Baya da haka akwai ƙungiyoyin matasa da muke da su a unguwa da yake muna cikin iyayen ƙungiyar mukan ba su shawara da su gujewa harkar shaye-shaye ta’addanci dabanci faɗa da halaye na rashin ɗa’a kuma suna bin abinda muke faɗa musu suna ɗaukar shawarwarin mu wannan ke nan.

Me za ka ce game da yadda za ka ga yaro ko yarinya ba sa zuwa makaranta wasu ma suna zuwa ɗin amma idan lokacin zana jarrabawa a sami wani ya zana musu, ta ya hakan yake faruwa ku a ɓangaren ku ya abin yake?

To ni dai gaskiya kin san in ana maganar wannan gaskiya ba mu cika samun irin wannan ba, tunda mu ba a ɓangaren secondary muke ba, ba mu samu irin wannan ƙalubalen ba, kullum cigaba ake yi ana kawo sauyi a harkar jarrabawa. Wani ma idan ba ka kan kujerarka ana iya ganewa, batun ka ɗauko wani ya zo yayi maka jarrabawa zai yi wahala. Mu dai gaskiya ba ma samun irin wannan matsalolin a nan gefen ƙwarai da gaske.

Ta ya kake kallon Nijeriya a jiya da kuma yau?

Maganar gaskiya Nijeriya jiya da yau sam sam ba za ta haɗu ba, jiya ta zo ta tafi yau muna cikin ta gobe kuma sai Allah.

To yanayin rayuwar fa?

Ta canja ana cikin iftila’i musiba da bala’i, kuɗi ya yi wahala in ma akwai shi ba shi da albarka in kuma ka samu, to abu ɗan kaɗan za ka iya siya da kuɗi mai yawa. To kin ga matsalar ba mu da gwamnatin kenan wacce zata tausaya wa mutane hatta masu kuɗin kuka suke yi balle kuma ma’aikacin gwamnati ko ƙaramin ɗan kasuwa.

Ko ta wacce hanya kake ganin mutane za su bi domin su sami sauƙi?

Hanya ɗaya idan har gwamnati za ta tsaya ta saurari abinda mutane suke faɗa, to rashin sa’ar da aka yi ita wannan gwamnatin ba ta sauraren mutane, taki tsaya wa ta ji koken talakawanta, ra’ayin kanta kawai take yi. 

Ke nan kana ganin cewar mu ɗin tamkar bayi ne  a gare shi domin manyan mu na Arewa sun riga sun siyar da mu?

To daman ai siyenmu ya yi kuma dukanmu muna da laifi ya kamata a tsaya a canja tsarin yadda ake zaɓen Nijeriya kowa ya je ya yi karatun ta nutsu idan ɗan siyasa ya ɗauki kuɗi ya ba ka kada ka ƙi karɓa, ka karɓa in ka tashi ka zaɓi cancanta sannan don Allah idan mutane kai kuma suka zaɓe ka don Allah ka tsaya ka yi wa mutane abinda ya kamata idan ba haka aka yi ba kullum za mu yi ta tsayawa waje ɗaya ne.

Me kake so ga mutane?

Abinda nake so ga mutane shi ne mu tsaya mu kawo sauyin mulkin da ake yi a Nijeriya domin mulkin da ake yi a Nijeriya ba adalci ko kaɗan a cikin sa. Yanzu ki duba ki gani tsadar man fetur ɗin da aka sa mana, zumunci ma ya gagare mu, walwala babu ita a fuskokin mutane, mutanen da ka sani da masu ƙiba ne duk sun bi sun rame, wanda wani fargabar abinda zai siyo ya siyar ba ma wai ya ci ba, ita ke sa shi rama, domin idan yanzu ka siyo abu dubu ɗaya an jima da ka koma an ƙara masa dari biyar ko ma fi. Mutane sun bi sun zabge, mutane sun zama talakawan ƙarfi da yaji, mutane sun zama abin tausayi. Wallahi idan na kalli wasu cikin abokanaina ba na iya gane su, waɗanda ba su shirya yin furfura ba duk sun bi sun furfure ta ko’ina, kuma ba wani abu ba ne ya jawo haka yunwa ce, mutum ne idan ya ɗauki albashinsa sai ki ga kuɗin ba zai isa ya ci da iyalinsa ba bare kuma a kai ga ya sawa mashin ɗinsa mai domin fita zuwa wurin aiki. Yanzu taro muka zo amma motocinmu duk mun aje su a gida, mun hawo motar haya yanzu daga Kaduna zuwa Zaria sai ka sha man dubu goma sha biyar wanda a da man dubu goma sha biyar zai cika min tanki taf har ma ya zo yana zuba, ana ta waƙar za a ƙara mana albashi amma har yanzu ba a ƙara mana albashi ba. Don haka nake kira da babbar murya ga talawa da mu canja, mu sani ɗan abinda za a ba mu ba zai kai ga ko makogwaranmu ba ballantana ya isa cikinmu har mu sa ran zai ƙosar da mu na awanni. Gaskiya wannan ƙasar muna buƙatar shugabanni masu sauraremu, a daina siyen ƙuri’a kuma a daina ba da kuɗi. Idan aka sauraremu kuma ayi mana abinda muke so, ƙin yin hakan wallahi muna nan kullum jiya iyau abinda ba mu fata, kada a zo a wayi gari talaka ya tare mai kuɗi a hanya ya ce zai ƙwaci abinci a hannunsa. Allah ya kiyaye saboda idan yunwa tai yunwa fa babu babba babu yaro ba mai kuɗi ba talaka babu shugaba babu saraki ba za a tsaya a ce a’a wannan wane ne ba sai dai a yi kan mai uwa da wabi. Kwanakin baya an yi zanga-zanga ba ta yi tasiri ba, amma mu tsoron da muke kada nan gaba zanga-zanga ta kufce ta fada hannun wadanda bai kamata ba, to idan fa aka ci gaba da yin shiru abin zai ƙara girmama. Kirana ga gwamnati ta tsaya ta saurari ihun da muke yi a dawo da mai lita ɗari biyu ana dawo da litar mai komai zai koma yadda yake, kuma gwamnati ta biya mana tallafin domin dukiyarmu ce. Bature ya ce (domocaratike is goɓernment of the people by the  for of the people ) kuma ai gwamnatin tamu ce kuma abinda muke so ya kamata a yi mana, ba wai ra’ayinsu za su dinga yi mana ba, su daina mana ra’ayinsu tunda mu muka zaɓe su a dawo da mai lita ɗari biyu, a ɗibi kuɗin namu a dinga tallafi da shi, mun yarda mu mun fi son haka ana cire tallafi kuɗin makaranta zai dawo, abinci zai sauƙaƙa, rashin tsaro zai kau, kuɗin yadi da aka dinka wa na ‘yan makaranta zai sauka, komai zai sauka amma ƙin yin hakan din ba zai sa a sami yadda ake so ba saboda me? Abubuwa sun yi tsada, tsadar kaya haraji ya yi tsada, kuɗin haya yai tsada, kuɗin mota ya yi tsada, siyen motar ma tsada, to ta ya za a yi rayuwa tai kyau? Rayuwa sam ba za ta yi daɗi ba saboda haka janye tallafin kuɗin mai da aka yi mana, duk shi ya janyo mana wannan bala’in dan haka ni inna kira ga gwamnati lallai lallai a koma inda aka fito. Yin hakan shi zai sa abubuwa su daidaita, domin wannan shi ne ummul aba isun matsalar da take fuskantar Najeriya, don haka muna kira da babbar murya don Allah don darajar Annabi shugabanni su tsaya su saurare mu.