Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Argungu da Augie Honarabul Sani Yakubu Ƴargiwa ya yi kira ga ƴaƴan jam’iyyar ADC da su ajiye duk wani bambance-bambance su zo a haɗu don fuskantar zaɓe mai zuwa.
Ya yi wannan kira ne a garin Argungu a wani taron shugabannin jam’iyyar na ƙaramar hukumar Augie.
Honarabul Ƴar Giwa ya ce a jam’iyyar ADC babu wani bambanci ga dukkan ƴan takarar da aka tsayar tun kama daga ƴan majalisar dokoki, tarayya, dattawa da gwamna da kuma shugaban ƙasa.
ADC ɗaya ce kuma mai manufa ɗaya saboda haka yanzu abinda ke gaban kowa shi ne yadda za a fuskanci gwamnati duk da ya ke kowa ya san ba aiki ne mai sauƙi ba amma cikin ikon Allah za a yi nasara musamman irin wannan gwamantin da ke azabtar da al’umma da yunwa da talauci uwa-uba ga rashin tsaro wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane musamman a wannan yankin na Arewa.
Lokaci ya yi da kowa ya ajiye bambance-bambancen ra’ayin tsayar da ƴan takara, wannan tsari ne na Allah kuma haka ya tsara ba wani mahaluki da ke iya canja hukuncin Allah.
