Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Janar Manaja na masaukin baƙi na Porto Golf Hotel, Mista Oliver Jonathan, ya bayyana cewa kamfanin ya bai wa ma’aikatansa tallafi na musamman domin taimaka musu a lokacin azumin watan Ramadan.
Jonathan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Kano a ranar Litinin, inda ya ce kamfanin ya ɗauki matakin ne domin sauƙaƙa wa ma’aikata gudanar da ibadarsu cikin kwanciyar hankali a wannan wata mai alfarma.
Ya ce daga cikin tallafin da aka bai wa ma’aikatan akwai rage lokutan aiki na wasu awanni, samar da abincin buɗa-baki, da kuma wasu tallafi da suka shafi bukukuwan Sallah kamar yadda kamfanin ya saba yi a kowace shekara.
A cewarsa, wannan mataki wani ɓangare ne na tsarin kula da jin daɗin ma’aikata da kamfanin ke da shi, domin tabbatar da cewa ma’aikata suna aiki cikin yanayi mai kyau da gamsuwa.
Haka kuma Janothan ya ƙara da cewa kamfanin na ba da tallafi ga al’umma ta hanyar shirin Corporate Social Responsibility (CSR), inda ba ma’aikata kaɗai ba har da wasu daga cikin al’umma ke amfana da irin waɗannan tallafi a lokuta daban-daban.
Ya yi kira ga sauran kamfanoni da cibiyoyi masu zaman kansu, musamman masu hannu da shuni, da su ƙara zage damtse wajen taimaka wa al’umma a wannan lokaci na watan Ramadan, domin rage wa masu ƙaramin ƙarfi radadin rayuwa.
A ƙarshe, Janothan ya yaba wa gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa ƙoƙarin da take yi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.
Ya ce wannan zaman lafiya ne ya sa Kano ta ci gaba da kasancewa cibiyar kasuwanci da karɓar baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Haka kuma ya yabawa Hukumar Kula da Yawon Buɗe Ido da Shaƙatawa ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Tukur Bala Muhammad Sagagi kan irin haɗin kan da suke ba wa kamfanoni masu zaman kansu.
Janothan ya bayyana cewa kafa Porto Golf Hotel ya taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasa tare da ƙara bunƙasa harkokin yawon buɗe ido da karɓar baƙi a jihar Kano.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu, ‘yan kasuwa, cibiyoyin ilimi, hukumomi da sauran baƙi daga sassa daban-daban na ƙasa na amfani da wannan wuri wajen gudanar da taruka da kuma samun masauki a duk lokacin da suka ziyarci birnin Kano.
