Magidanci ya yanke marainansa yana tsaka da sharar barci

Wani manomi a ƙasar Ghana mai suna Kofi Atta, ya tsinci kansa a asibiti a cikin wani mawuyacin hali bayan da ya yanke marainansa a lokacin da ya ke tsaka da sharar barci.

Atta, ya shaida wa manema labarai a kan gadon jinya yadda lamarin ya faru daki-daki, inda likitoci ke ta ƙoƙarin duba yadda za su yi masa aiki.

Ya ƙara da cewa, a yanzu dai ana masa ƙarin ruwa ne tare da wasu allurai, amma duk da haka sai an yi masa tiyata.

Ya ci gaba da cewa, a yanzu ba ya da ko kuɗin da zai biya motar asibitin da za ta ɗauke shi zuwa Asibitin Koyarwa na Komfo Anokye, da ke Kumasi a Ghana, inda a can ne za a iya yi masa babbar tiyata.

Mutumin ya ce, yana barcin da rana ne a kan wata kujera sai ya yi mafarki cewa yana yanka nama a ajiye a gabansa, wanda zai dafa abinci da shi, inda a cikin barcin ya jawo wuƙa ya zabtare marainansa.

Atta ya ce, abin ya ba shi mamaki kwarai domin har lokacin da wasu makwabtansa biyu suka kawo masa agaji bai san me ya faru ba, sai da ya tashi daga kan kujerar ya riƙa jin wani zafi a gabansa ga kuma jini na zuba.

Ya ce, har lokacin da aka kawo masa ɗaukin ba ya tabbacin abin da ya faru, ji ya ke kamar yana mafarki ne.

Ya ƙara da cewa, shi kansa bai san yadda aka yi ya ɗauko wuƙar ba, ya ce, “abin ya ɗaure min kai.”

Manomin mai shekara 47 wanda ke garin Assim Akomfode a Ghan, bayan ya yanke marainan nasa a cikin barci har ya yi kururuwar neman taimako bai farka ba yana cikin mafarki ne domin shi duk bai san abin da ya faru ba a lokacin.

Ya ce, duk da cewa makwabtansa sun kai masa ɗauki inda ya riƙa jin zafi a gabansa ga kuma jini yana zuba, bai fahimci abin da ya faru ba, sai daga baya a gadon asibiti hankalinsa ya dawo ya gane abin da ya faru.

Ƙarin haske daga likitoci A fagen ilimin kula da lafiya, akwai wata larura da ake kira ‘Parasomnia’ a Turance, inda mutum kan aikata wasu abubuwa saɓanin na hankali a lokacin da ya ke barci.

Wannan larura takan sa mutum ya riƙa tafiya ko maganganu ko fitsarin kwance ko mugun mafarki ko ƙiƙƙifta ido da sauran abubuwa na daban-daban a lokacin da ya ke barcin.

A lokacin da mutum ya ke cikin wannan hali wasu da ke tare da shi ko kusa da shi za su ga kamar ba barci ya ke ba yana farke ne, to amma yana cikin barci ne bai san abin da ya ke yi ba.

Mutanen da ke cikin wannan yanayi ba sa iya tuna abin da ya faru da su ko abin da suka aikata a lokacin da suke cikin haka.

Bayanai sun ce abin da mutum kan yi a wannan lokacin kamar yana aikata abin da mafarkinsa ya ƙunsa ne a zahiri.