Jarirai na murmushi idan mai juna-biyu ta ci karas – Masana Kimiyya

Wasu ƙwararrun masana kimiyya sun gano cewa, ‘yan tayin da ke cikin mahaifa, na yin murmushi idan iyayensu suka ci karas, haka kuma suna yin fushi idan iyayen suka ci ganye wani iri.

Cibiyar binciken ‘yan tayi ta jami’ar Durham da ke Birtaniya, ta ce, binciken shi ne irinsa na farko da ya samu hujjar da aka naɗa ta na’urar ɗaukar hoton ciki da ke nuna yadda ‘yan tayin ke kasancewa lokacin da iyayensu ke cin abinci iri-iri.

An gudanar da binciken ne a kan mata masu juna-biyu fiye da 100 tare da jariran da ke cikinsu a Ingila.

An bai wa mata masu juna 35 kwayoyin da ke ɗauke da sinadarin karas, sai kuma 34 da aka bai wa awayoyin da ke ɗauke da sinadarin ganyen salak, a yayin da aka bar mata 30 ba tare da ba su komai ba.

Masu binciken sun wallafa rahotonsu a mujallar kimiyya cewa, minti 20 bayan da iyayen suka haɗiyi ƙwayoyin, wata na’urar ɗaukar hoton ciki mai suna 4D ta nuna yadda ‘yan tayin da ke cikin mahaifa da aka bai wa iyayensu qwayoyin da ke ɗauke da sinadarin ganye na murtuke fuska, alamar rashin jin daɗi.

Haka kuma na’urar ta nuna yadda ‘yan tayin ke murmushi bayan da aka bai wa iyensu ƙwayoyin da ke ɗauke da sinadarin karas.

Su kuma matan da ba a bai wa komai ba jariran da ke cikinsu babu abin da suka yi.

Binciken da suka gabata sun nuna cewa abincin ɗan adam yana farawa ne tun kafin a haife shi, sakamakon ganowa da aka yi cewa ruwan da ke gudana a jikin ‘yan tayin na ɗauke da sinadaran abinci daban-daban, ya danganta da irin abincin da iyayensu ke ciki.

To amma wannan sabon binciken na Jami’ar Durham ya ce, shi ne bincike na farko da aka nuna yadda ‘yan tayin ke yi bayan cin abinci daban-daban da iyayensu suka yi.