Nijeriya ta maka Meta a kotu kan saɓa doka, ta nemi diyyar biliyan N30

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Kula da Tallace-tallace ta Nijeriya (ARON) ta maka kamfanin Meta, mamallakin Facebook da Instagram da kuma WhatsApp da abokin hulɗarsa AT3 Resources Limited, a wata Babbar Kotun Abuja.

Cikin sanarwar da ta fitar ran Talata, ARCON ta ce rashin kiyaye dokar amfani da intanet wajen tallace-tallace ya sanya ta maka kamfanin a kotu.

A cewar ARCON, tallace-tallacen da kamfanin Meta ke yaɗawa zuwa Nijeriya ta shafukasa na soshiyal midiya ba tare da kikaye ƙa’idojin da aka shimfiɗa ba hakan ya saɓa wa dokar talla ta Nijeriya.

ARCON ta ce Meta na yaɗa tallace-tallacensa a Nijeriya ba tare da an tantance ba wanda hakan ya sa Gwamnatin Nijeriya tafka asara wajen samun kuɗin shiga.

Don haka ARCON take neman a ci tarar Meta biliyan N30 sakamakon rashin kiyaye wannan doka.

Hukumar ta ce ba za ta lamunci take doka ba wajen yaɗa tallace-tallace a Nijeriya.