Buhari zai gabatar wa Majalisa kasafin 2023 ran Juma’a

Daga BASHIR ISAH

A ranar Juma’a ta wannan makon ake sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin 2023 na tiriliyan  N19.76 ga Majalisar Tarayya a  Abuja.

Buhari zai gabatar da kasafin ne a zauren wucin-gadi na Majalisar Wakilai da misalin karfe 10 na safe.

Kamfanin NNPC ya samu ribar biliyan N674 a wata 12
NAJERIYA A YAU: Yadda Ruwan Kasashen Ketare Ke Janyo Ambaliya A Najeriya

A baya an jiyo Babban Daraktan Ofishin Kasafi na Tarayya, Ben Akabueze na cewa a watan Satumba Shugaban Kasa zai gabatar da kasafin 2023 ga Majalisar Tarayya.

Akabueze ya ce an tsara kasafin 2023 ne daidai da tanadin dokokar Gwamnatin Tarayya da sauran ka’idojin da aka shimfida dandage da hakan.

Idan dai za a iya tunawa, a Disamba, 2021 Buhari ya sanya wa kasafin 2022 hannu na tiriliyan N17.127 bayan karin biliyan N735.85 da aka samu kan alkaluman farko.