Wakilin Sin ya ƙalubalanci Amurka da ta daidaita matsalar nuna bambancin launin fata a ayyukan ’yan sanda da sauransu

Daga CMG HAUSA

Wakilin Sin Jiang Duan ya shaida wa taron majalisar kare haƙƙin ɗan Adam ta MƊD karo na 51 da aka gudanar a jiya cewa, ’yan asalin Afirka dake Amurka, suna fuskantar yanayin nuna bambanci a ayyukan aiwatar da doka, don haka ya ƙalubalanci ƙasar Amurka da ta ɗauki matakai don daidaita matsalolin nuna bambancin launin fata, da tsauraran matakan da ’yan sanda suke ɗauka bisa bambacin launin fata da sauransu.

Jiang Duan ya yi nuni da cewa, ra’ayin mulkin mallaka, da cinikin bayi, sun haifar da ra’ayin nuna bambancin launin fata.

Kodayake wannan babi ya wuce a tarihin ɗan Adam, amma ra’ayin mayar da fararen fata a gaban wasu yana ci gaba da kasancewa.

Ya ce a ƙasar Amurka, ’yan asalin Afirka suna fuskantar yanayin nuna bambancin launin fata, da rashin daidaito gare su.

Bisa ƙididdigar da aka yi, yiwuwar samun mutanen ’yan asalin Afirka da ’yan sanda suke harbewa har lahira, ta fi ta fararen fata fiye da ninki biyu, kana yawan ’yan asalin Afirka da suke cikin kurkuku a ƙasar Amurka, ya fi na fararen fata har ninki shida.

Jiang Duan ya bayyana cewa, ƙasar Sin ta ƙalubalanci ƙasar Amurka, da ta ɗauki matakai, don daidaita matsalolin nuna bambancin launin fata, da tsauraran matakan da ’yan sanda suke ɗauka bisa bambancin launin fata da sauransu, da aiwatar da kudirin da aka tsai da a babban taron MƊD, da majalisar kare haƙƙin ɗan Adam ta MƊD.

Mai fassara: Zainab Zhang