Makaɗan Hausa: Alhaji Sa’idu Mai daji Sabon-Birni

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An haifi Alhaji Sa’idu Mai daji a garin Tara ta sarkin Kwanni, ita kuma Tara tana bin Sabon-Birni ta sarkin Gobir, jihar Sakkwato. Sannan mahaifinsa shi ne Mainasara. Ya kiyasta cewa yana da shekara arba’in da biyar (45), watau ke nan an haife shi a wajejen 1938.

Dalilin kiransa Maidaji shi ne, a lokacin rayuwar mahaifinsa suna zaune ne a tsohon garin Tara. Sai wata rigima da faɗace-faɗace ta haddasu tsakanin mutanen Tarar, sai aka yi ta tashi ana barin garin, bayan kuwa har sun yi shuka. Mahaifinsa Mainasara, ya ce shi kam ba zai bar shukarsa ta lalace a banza ba, sai dai a koma gona.

A gonar ya gyara wurin zama, suka zauna tare da sauran ’yan uwansa. Watau irin wannan zama shi ne ake cewa zaman gona. Ba sa zuwa gari wata ƙila sai ran kasuwa ko Juma’a. To, bayan da aka koma ne gidan gona aka haifi Maidaji, da ma an tafi da cikinsa yana tsoho. Daga nan, sai mahaifinsa ya ce: “An sami Maidaji”, watau ɗan gidan gona.

Suna nan zaune har Maidaji ya girma, sai ruwa ya malale wurin, ya rusa wasu ’yan gine-ginen da suka yi, sai mahaifinsa da shi da sauran iyalinsa suka bar gidan gona na Tara, suka koma Rambadawa. Rambadawa tana bin Sarkin Kwannin Tara ne, Tara kuma tana bin Sarkin Gobir na Sabon-Birni.

Ƙuruciyarsa:

Ba sai an ce maidaji ya yi noma ba, domin da jin yadda aka haife shi, da inda ya ke zaune bayan haihuwarsa, an san ya tashi cikin noma ne. Tun yana ƙarami ya ke noma, har ya shahara gare shi.

Bayan noma, ya taɓa karatun allo. Ya yi tafiye-tafiye don yawon makaranta. Ya je kamar Mai Lalle da Tsamaye. Yawanci Mai daji da abokansa sukan sauka a wajen wani Sarki ne ko Hakimi da suka tabbata yana da abinci.

Za su yi yarjejeniya da Sarkin cewa ya dinga ciyar da su, su kuwa su riƙa yi masa noma idan sun dawo daga aikin gona, sai su yi karatunsu na allo da ya kawo su. don haka, duk inda suka tafi ba sa yawon bara, kuma ya yi karatun yaƙi da jahilci tun farkon kafa shi a ƙauyensu, amma bai daɗe a ciki ba.

Waƙa da kiɗa:

Alhaji Sa’idu Mai daji; ya yi gadon kiɗa da waƙa ne. Domin mahaifinsa ya yi, kuma wansa Nadada shi ya ke yi. Hasali ma, shi ne makaɗa na garin. Sannan wani wansa kuma wanda ake kira Alhaji Mai gari yana yin kiɗan har yanzu.

Maidaji, ko da ya ke ya tashi cikin waqa bai koye ta a wajen mahaifinsa ba. Wansa Nadada hi ne ya yi tashen waƙa kwarai. Ya yi waƙoƙi da dama, sannan yana da basira da hikima a wajen shirya waƙoƙinsa.

Bayan haka, ya yi makarantar allo har ya sauke. Kuma shi ma ya yi karatun yaƙi da jahilci. Daga cikin ire-iren waƙoƙinsa akwai:

  • Kiɗan Noma.
  • Kiɗan Fada.

Ya yi tafiye-tafiye da dama zuwa garuruwa don waƙa. Daga cikin yaransa da ke amsa masa waƙa, akwai:

(i) Alhaji Maigari — kanensa ne

(ii) Na Gambo Roko — kanen tsohonsa ne

(iii) Marafa—kanensa ne

(iv) Sa’idu Mai daji—ƙanensa ne, mai kiɗan kanzagi

Fara waƙarsa:

Mai daji Sabon-Birni ya fara waƙa tun yana ɗan ƙarami. Yana bin yara ’yan uwansa gona, idan suna noma, shi ko ya dinga yi musu ’yan waƙe-waƙe. Daga nan ya fara zuwa da wasu yara suna amshi, wasu kuma suna kiɗa da gwangwani; sai kuma aka fara gayyatarsa ya je kiɗa na gayya.

Ya koyi kiɗa da waqa na sosai a wajen wansa Nadada. Kuma ya fara da kiɗan kurkutu ne, sai kuma ya shiga cikin masu amshi, kamar dai yadda ya gabata. Ko da ya ke Mai daji yana tare da wansa wajen kiɗa, amma yakan yi gayauna ya tafi ya dinga yi wa wasu mutane ’yan wake-wake a gona ko a kasuwa da sauran wurare.

Waƙar noma ta farko wadda ya yi, ita ce waƙar da ya yi wa Sarkin noma Arzika. Ita Ce:

Gindi: Sarkin yai abin daka ya huta,

        Zaki ɗan Abubakar ɗan Buda.

        Arzika jikan Salau Magajin Sanda,

        Bai ci amanar gida ba, balle daji.

        Arzika ɗan Imamu bawan Allah,

         Bai ci amanar gida ba balle daji:

Bayan wannan waƙa ya ci gaba da yin waƙoƙin noma.

Kafin makaɗa Nadada ya bar waƙa, sai da Mai daji ya san wani abu dangane da dabara da hikimar shirya waƙa. Ya kai fagen ya yi jagorancin waƙa. Bayan rasuwar Makada Nadada sai Sa’idu Maidaji ya haye khalifarsa. Ya ci gaba da shugabancin waƙa. Yanzu ma shi ne makaɗan garin Rambadawa, ko da ya ke sarkin Gobir na Sabon-Birni yana son ya koma wajensa.

Ire-iren waƙoƙinsa:

Bayan da Maidaji ya hau gadon shugabancin waƙa sai ya kiƙa yin waƙoƙin fada, gami da maimaita waɗanda wansa Nadada ya yi. Sai ya kasance yana irin waɗannan kaɗe-kaɗen ne:

(i) Kiɗan noma (manoma)

(ii) Kiɗan Fada (Sarakuna)

(iii) Kiɗan Siyasa

(iv) Kidan Jama’a (talakawa).

Tsara waƙarsa:

Maidaji yakan sami bayanan da zai shirya waqa da su ta waɗannan hanyoyi:

Samun bayanai daga wajen waɗanda zai shirya wa waƙa su kansu.
Samun bayanin Sarki ko hakimi daga bakin talakan garin ko Bafadensa Yakan tambayi nasabar Sarkin, iyayensa da kakanninsa.

Maroƙansa, watau yana aiken marotinsa ya tambayo bayaflifl mutumin. Ko kuma bayanin wanda ya yi masa kyauta a lokacin da ya ke yin waƙa.

Maidaji kuma yakan yi wa wani waƙa saboda:

irin bajinta da ƙoƙari ko himma da manomi ya nuna. Waɗannan halaye sukan sa ya yi wa mutum wada ko bai neme shi da yin haka ba. Ko kuma idan shi kira shi da ya yi waƙar.

Yakan tsara waƙoƙinsa ta waɗannan hanyoyi. Ya tsaya gida ya shirya wada a natse.
Wannan kuwa yakan tsara ta inda duk ta samu.

Yaransa ’Yan amshi/mataimaka;

Mafi yawan yaransa daga kannensa, sai kanen tsohonsa, sai wansa, sai kuma ’ya’yansa, kamar yadda aka bayyana a baya, dama gidansu gidan waƙa ne. Ga sunayen yaran:

(i) Tanko Ibrahim kanen mahaifinsa ne.

(ii) Alhaji Mai Gari — wansa ne

(iii) Hana — ɗansa ne

(iv) Baciri — ɗansa ne

(v) Abara — ɗansa ne

(vi) Sallau – ɗansa ne

(vii) Garba na mai kosai ɗansa ne

(viii) Dogo — ɗansa ne

(ix) Dan Malam — ɗansa ne

(x) Ibrahim — maroƙinsa kuma baransa ne.

Waɗanda ya ke yi wa waƙoƙin noma:

Mai daji yana yi wa kowane manomi waƙa, musamma ma wanda ya nuna kwazo da bajinta da kuma wanda ya masa wata gagarumar kyauta ta ƙasaita.

Maidaji Sabon-Birni ya shahara sosai dangane da waƙa musamman ma waƙoƙin noma. Waƙoƙin Mai daji na Sabon-Birni. sun kai wurare da yawa. Akan sa su gidajen Rediyo, musamman Rediyon Rima, Sakkwato da na Tarayyar Nijeriya a Kaduna. Sannan kuma akan sa su Gidajen Rediyo masu hoto, da sauran wurare.

Malamai da ɗalibai daga Jami’o’i daban-daban sukan same shi har gida don bincike a kan waƙoƙinsa. Mai daji ya yi waƙoƙi da dama fiye da waƙoƙi (1,000), na waƙoƙin noma da waƙoƙin sarauta da na sauran talakawa.

Maidaji yana da mata uku da kuma ’ya’ya shida duk kuma rayayyu, a garin Rambadawa kilomita ishirin da biyu (22) daga sabon-Birni kuma tafiya ce ta rairayi da burji, ba kwalta ba.