Mahajjata kusan miliyan biyu suka kammala aikin Hajjin 2025

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An kawo ƙarshen aikin Hajjin bana a ranar Litinin, 13 ga watan Dhul Hijjah, daidai da ranar 9 ga watan Yuni, inda Musulmi sama da miliyan 1.6 daga ƙasashe fiye da 150 suka halarci aikin hajjin na bana.

Kwamitin Aikin Hajji da Umrah na Saudiyya ne ya sanar da kammala aikin a Mina, inda aka bayyana cewa babu wata matsala da aka fuskanta. 

A ranar Litinin, mataimakin sarkin yankin Makkah, Yarima Saud bin Mishaal, wanda ya bayyana haka, ya yaba wa shugabannin masarautar da suka tabbatar da ganin an gudanar da aikin hajjin lami lafiya.

Yayin da hukumomin suke tabbatar da cewa masarautar da shugabancinta na alfahari da yadda aka tafiyar da aikin hajjin cikin kwanciyar hankali da kuma nasara, sun bayyana cewa an fara shirye-shiryen Hajjin 2026 nan take.

A bana mahukuntan Saudiyya sun kafa wasu matakai da suka haɗa da abubuwan more rayuwa da tsaro da lafiya, da nufin tabbatar da cewa mahajjata sun yi aikin hajji karɓaɓɓe.

Yayin da aikin Hajji na 2025 ya zo ƙarshe, hukumomi sun sanar da cewa ba a sami wasu manyan matsaloli na lafiya, tsaro, ko kuma ayyukan da suka shafi hidima ba.

Wasu alhazan Nijeriya da suka halarci aikin hajjin sun bayyana wa gidan talabijin na Channels da ke Mina abin da ya faru da su.

Wani mahajjacin Nijeriya daga jihar Osun, Muritala Fakunle, ya ce, “Hajjin bana ya fi na bara tasiri sosai ga mahajjata, an yi amfani da kayan aiki da yawa, dole ne in shaida muku a Mina, Muzdalifah, da Arafat, muna da karin kayan aiki, gadaje da sanyaya suna da inganci.

“A wannan shekarar, mutanen da suka zo nan a bara kuma suka zo a wannan shekara, za su san cewa wannan shekara ita ce babbar shekara.”

Wani alhajin Nijeriya daga jihar Katsina, Nasir Yahaya, ya bayyana irin waɗannan kalamai, inda ya ce, “Ayyukan aikin Hajjin bana na 2025 sun ba da ma’ana, babu wata matsala ga alhazan Nijeriya, kashi 100 na abinci, ayyukan, har a Mina, suna da kyau, ba kamar da ba, ba kamar bara ba, wannan shekarar ta yi kyau, babu cinkoso a masaukai.

By ukarofi