Mai gidan haya ya shiga hannu a Nasarawa bayan halaka ɗan hayarsa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia 

Wani mai gida da aka san shi da suna Samson kadai a yanzu haka yana hannun ‘yan sanda a Masaka ƙaramar hukumar Karu ta Jihar Nasarawa kan zargin kashe ɗan hayar gidansa.

Marigayi ɗan hayar mai suna David Runyi Osim daga Usumutong a Jihar Kuros Riba, an ce an soke shi da wuƙa har ya mutu.

Osim ya zauna a gidan tare da matarsa na ƙasa da watanni shida kafin mutuwarsa.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai bayyana cewa mamacin ya mutu ne sakamakon sara da wuƙa ba dukan adda ba.

Da yake ba da labarin abin da ya faru, wani dangin mamacin, Samuel Okun, ya ce Osim ya dawo ne daga Maiduguri bayan ya kammala aikin gini.

Yace wani abokinsa da ke aiki a Abuja ne ya gayyace shi ya zo ya zauna a Masaka.

A cewarsa, Osim ya kwana a otal na kimanin wata ɗaya yayin da mai gida da iyalinsa suka fita daga gidan ɗakuna uku, bayan haka ya koma cikin boys’ quarters da ke bayan ginin.

Okun ya bayyana cewa a ranar Juma’ar da lamarin ya faru, matar Osim ta je kasuwa don siyan kayan abinci kuma ta ji rauni a hannunta a kan hanyarta.

Osim, a cewarsa, ya kai ta inda aka ɗinke mata raunin. Da suka dawo gida, suka dafa abinci suka ci tare da mai gida a cikin ɗakin su.

Bayan kamar minti 10 zuwa 15 da Osim ya gama cin abinci, mai gidan ya ce ya ƙwanƙwasa ƙofarsa ya ce ya fito ya ga wani abu.

Osim, wanda ba shi da wata saɓani da mai gida a baya, ya fito sanye da gajeren wando kadai.

Okun ya zargi cewa da zarar Osim ya shiga falon mai gida, mai gidan ya far masa da wuƙa.

An ce Osim ya yi ihu, ya kuɓuce ya fita da gudu, amma mai gidan ya bi shi.

Matarsa, wacce ta fito da jin muryar mijinta, ta tarar da shi yana zubar da jini sosai. An ce mai gidan ya ci gaba da kai masa hari kafin ya yi tsalle ya ƙetare katanga ya shiga wani daji da ke kusa bayan ya fahimci ya kashe wanda ya kai wa hari.

Maƙwabta da suka ji matar na kukan neman taimako sun garzaya wurin. Okun ya ce da suka isa, sun tarar da Osim a kwance babu rai a ƙasa.

Sun bi mai gidan, sun kama shi suka tambaye shi, amma ya ce bai san abin da ya faru ba ko dalilin da ya sa ya kai masa hari.

Daga baya matar ta hau keken da aka aro don sanar da ɗan uwan Okun, kuma da suka dawo, Osim ya riga ya mutu. An kira ‘yan sanda, an kama wanda ake zargi, kuma an kai gawar asibiti.

Okun ya ce an kai gawar zuwa Maitama Medical Center da misalin ƙarfe 12 da wani abu.

Ya ce da ya je ɗakin ajiye gawa tare da matar da wasu ‘yan uwa a ranar Asabar, ba a ajiye komai ba, kuma sai da ya biya N90,000 don adana gawar.

A Ofishin ‘yan sandan Masaka, jami’in ‘yan sanda mai kula da sashen ya ce za a miƙa lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar, CID, da ke Lafia, saboda ya wuce abin da sashen zai iya gudanarwa.

Okun ya ce yana nan lokacin da wanda ake zargi yake bayar da bayaninsa a tashar. Ya ce wanda ake zargin na ta cewa “babu komai” lokacin da aka tambaye shi ko sun yi saɓani, ko Osim ya sace masa wani abu, ko kuma abin da ya faru da gaske.

Ya ce DPO ɗin daga baya ya gaya musu cewa wanda ake zargin ya yi bayanin ikirari yana mai cewa ya kashe Osim. Okun ya ce wanda ake zargin ya kuma amince da hakan a gabansa.

Da yake tabbatar da lamarin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa, SP Ramhan Nansel, ya ce mamacin ba dukan adda aka yi masa ba, sara da wuka aka yi masa.

Okun yace Osim ya bar mata da ɗa ɗaya wanda ba ya zaune tare da su. Yace a yanzu iyalin ba sa neman wani abu sai dai adalci ga ɗan uwansu.

By ukarofi

Leave a Reply