Mai Kaltungo ya kai ziyarar godiya ga Sarkin Haɗeja

Spread the love

Daga  RABIU SANUSI a Kano

Uban ƙasa Mai Martaba Injiniya Saleh Muhammad Umar, (Mai Kaltungo) tare da wata tawaga mai ƙarfi daga Masarautar Kaltungo, sun kai ziyarar girmamawa da godiya zuwa Fadar Sarkin Haɗeja a Jihar Jigawa, HRH Dr. Adamu Abubakar Maje Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa.

Tawagar ta kunshi manyan hakiman Masarautar Kaltungo, ciki har da Magayakin Kaltungo wanda shi ne Shugaban Kwamitin Shirye-shiryen Bikin Baje Kolin Al’adun Masarautar Kaltungo na shekarar 2025, Madugun Kaltungo, Sa’in Kaltungo, Cikasoron Kaltungo, Sarkin Rafin Kaltungo, Jarumar Kaltungo, Malafan Kaltungo, da sauran manyan fadawa.

Ziyarar ta biyo bayan amsa gayyatar da Sarkin Hadejia ya yi na halartar Bikin Baje Kolin Al’adun Masarautar Kaltungo na shekarar 2025 a matsayin Uban Taro, inda ya aike da manyan wakilai domin wakiltarsa.

A wannan karo Mai Kaltungo ya jagoranci wasu daga cikin Kwamitin Shirye-shiryen bikin, karkashin jagorancin Magayakin Kaltungo Mr.Moh’d Dantata Ndus, domin isar da sakon godiya ga Sarkin Hadejia a madadin al’ummar Masarautar Kaltungo.

Da yake jawabi, Sarkin Hadejia ya nuna matukar jin dadinsa da wannan ziyara, yana mai yabawa Mai Kaltungo bisa jajircewarsa da kuma yadda ya jagoranci tawaga mai karfi duk da wahalar tafiya da daukar nauyin da ya rataya a kai, domin nuna godiya. 

Basaraken ya kuma tabbatar wa al’ummar Masarautar Kaltungo cewa Masarautar Hadejia na shirin kai ziyara ta musanya zuwa Kaltungo nan gaba kadan.

A ƙarshe, an yi addu’ar Allah Ya kara wa iyayen kasa lafiya, nisan kwana da ci gaba da zaman lafiya a masarautunsu.

By ukarofi