Shugaban KAROTA ya nemi haɗin kan jama’a don inganta tsarin zirga-zirga a Kano

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Darakta Janar na Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) Injiniya Faisal Mahmud ya yi kira ga al’ummar jihar da su ba hukumar cikakken haɗin kai domin ta samu damar aiwatar da ayyukanta yadda ya kamata wajen tabbatar da tsari da tsaro a kan hanyoyi.

Injiniya Faisal Mahmud ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano, inda ya jaddada ƙudirin KAROTA na kare rayuka da dukiyoyin jama’a ta hanyar tabbatar da bin dokokin zirga-zirga a faɗin jihar.

Ya ce haɗin kan direbobi, masu motocin haya da masu ababen hawa gaba ɗaya na da matuƙar muhimmanci wajen rage haɗurran mota, inganta lafiyar zirga-zirga da kuma sauƙaƙa motsi a birane da ƙauyukan Jihar Kano.

Shugaban hukumar ya kuma fayyace cewa KAROTA ba ta da manufar tsangwama ko gallaza wa kowa, illa tabbatar da bin doka da oda a ɓangaren sufuri. Ya bukaci jama’a da su fahimci manufofi da dokokin hukumar tare da mutunta jami’anta yayin da suke bakin aiki.

A ƙarshe, Injiniya Faisal Mahmud ya tabbatar da cewa KAROTA za ta ci gaba da ƙara wayar da kan jama’a tare da haɗa kai da sauran hukumomi masu alaka domin gina ingantaccen tsarin kula da zirga-zirga wanda zai amfani al’ummar Jihar Kano baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa ci gaba da samun haɗin kai tsakanin jama’a da hukumar zai taimaka matuƙa wajen samar da hanyoyi masu tsaro da kuma kyakkyawan tsarin sufuri a jihar.

By ukarofi