
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta janye sanarwar tsige tsohon Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdulsalam a hukumance.
Janyewar ta biyo bayan kudirin da shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini, ya gabatar a zaman majalisa karkashin jagorancin Kakakin Majalisa, Jibril Isma’il Falgore.
Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan zaman, Hussaini ya bayyana cewa bisa tanadin doka ta 3, Ka’ida ta 6A, ya yanke shawarar janye kudirin ne sakamakon murabus da tsohon mataimakin gwamnan ya yi da kansa.
Ya ce: “Mun janye dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, kuma an rufe batun gaba daya. Ba za mu ci gaba da bin wadannan zarge-zargen ba, domin aikinmu ya takaita ne wajen tsige jami’i idan aka same shi da laifi. Tun da ya yi murabus da kansa, ta yaya za mu ci gaba? Mu ba EFCC ko ICPC ba ne; mun cika aikin da aka dora mana.”
Wannan ci gaba ya zo ne bayan da Majalisar dokokin Jihar Kano ta fara shirin tsige Aminu Abdulsalam a ranar 5 ga Maris, 2026, bisa zargin aikata manyan laifuka, ayyukan almundahana da kuma rashin bin ka’idojin aiki.
Matakin ya biyo bayan wata bukata daga bangaren zartarwa, wadda ta bukaci majalisar da ta dauki mataki kan mataimakin gwamnan bisa zargin wasu kura-kurai a lokacin da yake kwamishinan kananan hukumomi tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024.
