Daga AISHA ASAS
Kafin komai bari mu fahimci ita kanta garin shinkafa wadda za mu shimfiɗa darasin namu kai.
Menene garin shinkafa?
Garin shinkafa ana yin sa ne ta hanyar niƙa ƙwayar shinkafa ta zama gari. Amma ba dukkan garin shinkafa ne iri ɗaya ba. Yadda aka sarrafa shi na iya shafar amfaninsa.
Shinkafa na da sassa uku:
Fatar waje mai ƙarfi.
Tsakiyar wadda wasu ke kira da tsakiyar rai
Farin ɓangaren ciki.
A duk waɗannan da na lissafa sashen waje shi ne mafi ɗauke da sinadarai masu kariya ga fata tare da kawar da wasu matsaloli kamar na rage kumburi.
Idan mun fahimta zan so mu wuce zuwa ga tambayar mu ta ko garin shinkafa na da amfani ga fata?
An jima ana faɗar cewa garin shinkafa na hidimtawa fata kamar haka:
1.Rage duhun fata.
2. Goge matattun ƙwayoyin fata.
3. Kare fata daga hasken rana.
4. Saka maiƙo mai yawa a fata.
Saidai masana sun ce har yanzu babu wani cikakken bincike da ya tabbatar da cewa garin shinkafa kaɗai na da wannan tasiri.
Wasu sinadarai da ake samu a ɓangaren waje na shinkafa (ɓawan shinkafa) su ne kamar haka:
Kariyar fata daga lalacewa.
Taimakawa wurin sabunta ƙwayoyin fata.
Rage kumburi.
Sai dai yawancin kayayyakin shafawa ba sa amfani da garin shinkafa kai tsaye; suna amfani ne da tsantsar sinadaran da aka tace daga shinkafa.
