Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar Hon. Abduljalal Haruna Runka, ɗan majalisar mai wakiltar karamar hukumar kankiya Hon. Salisu Hamza Rimaye ya bayar da ƙuduri a gina dam ga al’ummar garin Dan-nayaki dake ƙaramar hukumar, duba da garin sun kasance manoma ne na kayan mar-mari.
Haka zalika ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kaita Hon. Surajo Abdu Kwaskwaro ya nemi majalisa da ta amince da samar da ruwan sha a garin Kuntu da kuma gyara hanyar shiga karkara a garin Gwanga a mazaɓar Dankama ƙaramar hukumar Kaita.
Ƙudurorin sun samu cikakken goyon baya ga sauran ‘yan majalisa.
Daga ƙarshe majalisar ta amince tare da umartar akawun majalisar ya tura zuwa sashen zartaswa.
Haka kuma majalisar ta fara zaman sauraren kasafin kuɗin ƙananan hukumomi 34 da ke jihar.
