Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya naɗa Tunji Disu a sufeto janar na ‘yan sanda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Tunji Disu, wanda Mataimakin Sufeto Janar ne, a matsayin Sufeto Janar na rundunar ‘yan sandan Nijeriya.

Hakan na nufin an maye gurbin Kayode Egbetokun da shi a muƙamin.

An ruwaito cewa, cire Egbetokun ta matsayin ya faru ne bayan da Shugaba Tinubu ya nemi ya yi murabus a wata ganawa da shi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a jiya Litinin.

A ranar 19 ga Yunin 2023 Tinubu ya naɗa Egbetokun a matsayin Sufeto Janar na 22 a rundunar.

Kamar yadda a ranar 4 ga watan Satumbar 2024 ne ya yi daidai da lokacin ritayar Egbetokun kasancewar ya kai shekaru 60, saidai an ƙara matsa wa’adi bayan wani umarni akan hakan daga Shugaban ƙasar.

A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Egbetokun ya yi murabus ne saboda wasu dalilai na cikin iyalansa da ya dace ya mayar da hankali akansu, kamar yadda Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya bayyana wa jaridar PUNCH a yau Talata.

By Babaji