Majalisar Dokokin Ribas ta ƙuduri aniyar binciken kantoman riƙo Ibok-Ete Ibas

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wani sabon rikici na neman kunno kai a jihar Ribas da ke Kudu maso Kudancin Nijeriya, bayan da ‘yan majalisar dokokin jihar suka ƙuduri aniyar gudanar da bincike kan harkokin kuɗi na gwamnatin a tsawon watanni shida ƙarƙashin jagorancin ɓice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), da ya jagoranci jihar bayan Shugaba Tinubu ya kafa dokar ta-ɓaci a jihar.

Ana ganin cewa matakin da ‘yan majalisar suka ɗauka zai iya janyo takun saƙa tsakaninsu da tsohon kantoman riƙo na jihar, wanda a halin yanzu ake bin bahasin aikinsa.

Majalisar ta jaddada cewa huruminta ne ta gudanar da bincike kan harkokin kuɗaɗen jihar, wanda Ibok-Ete-Ibas ya ce ba huruminsu ba ne.

Sanarwar da Majalisar Dokokin jihar Ribas ɗin ta fitar game da shirin binciken tsohon kantoman riƙon na neman sake tayar da wata rikita-rikitar siyasa inda wasu ‘yan jihar suka ce dama suna jiran wannan rana ta zo.

A na sa ran binciken zai bi bahasin yadda Ibas ya tafiyar da harkokin kuɗaɗen jihar a lokacin dokar ta-ɓaci da aka sanya a jihar.

Binciken da ‘yan majalisar suka ayyana gudanarwa kan Ibas, ya samo asali ne daga zarge-zargen rashawa da kuma gurgunta ƙananan hukumomin jihar a lokacin da ya ke riƙon ƙwarya ciki har da bijirewa umarnin kotu da ta hana shi naɗa shugabannin ƙananan hukumomi 23 na riƙo a jihar.

ƙungiyoyin farar hula daga shiyyar Naija Delta sun nemi a gudanar da bincike kan ɓice Admiral Ibok-Ete Ibas, bisa zargin yin amfani da ƙarfin mulki da kuma karkatar da kuɗaɗen jama’a.

Matakin da suka ɗauka na binciken Ibas dai na ci gaba da haifar da cece-ku-ce, inda wasu kungiyoyi farar hula ke yabawa gwamnatinsa kan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, yayin da wasu kuma ke sukar gwamnatinsa bisa zargin kin aiki da abin da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada.

Alhaji Yahaya Wunti, me bibiyar dambarwar siyasar jihar ta Ribas ne da ma yankin Naija Delta, ya shaida wa Manhaja cewa, majalisar dokokin jihar ta Ribas ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin jin bahasin abin da aka yi da maƙudan kuɗin da jihar ta samu a tsawon watanni shida na mulkin Ibas.

Ya ce,” Kuɗin da jihar ta samu sun kai kusan naira biliyan dari biyu da hamsin da wani abu, kuma a yadda al’ummar jihar da ma ‘yan majalisar dokokin jihar ke fada manyan ayyuka na raya ƙasa da dama sun tsaya ba wanda aka ci gaba tun barin Gwamna Fubara mulki.”

Alhaji Yahaya Wunti, ya ce,” Akwai ma waɗanda ke cewa albashin watan Agusta da ya gabata ma sai da gwamna Fubara ya dawo kan mulki ya bayar da umarnin a biya, sannan kuma akwai masu maganar cewa an yi almubazzaranci da kuɗi wajen yin wasu ayyuka kamar misali sanya kyamarori na tsaro a gidan gwamnati sai da aka ware naira biliyan 22.”

Yanzu haka dai tsohon kantoman riƙon jihar ta Ribas, Ibok-Ete Ibas, ya yi watsi da

binciken, inda ya bayyana shi a matsayin wani aiki na wauta, sannan kuma ya cewa ‘yan majalisar ba su da hurumin bincikensa, bisa la’akari da cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ne ya naɗa shi.

Masana harkokin siyasa dai na cewa ba a bin mamaki ba ne idan sakamakon binciken ya yi matukar tasiri ga siyasar jihar Ribas da kuma sahihancin gwamnati mai ci kan binciken gwamnatin riƙon ƙwaryar.

Ana sa ran binciken zai yi ƙarin haske kan yadda ake tafiyar da harkokin kuɗaɗen jihar a zamanin Ibas.

Matakin da majalisar ta ɗauka na binciki Ibas ya sanya ayar tambaya kan yadda ake gudanar da ayyukan gwamnati.

Dokar ta-ɓaci, da aka sanya a jihar wani yunkuri ne na daƙile taɓarɓarewar harkokin siyasa da tsaro, inda wa’adin dokar ya kare a ranar 17 ga Satumba, 2025.

Masana na cewa wannan barazanar ka iya sake dawo da rashin zaman lafiya tun bayan kafa dokar ta-ɓaci a jihar.

By ukarofi