Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sakataren Jam’iyyar NNPP na ƙasa, Ogini Olaposi, ya ce, jam’iyyarsu ba ta cikin shirin da Sanata Rabiu Kwankwaso ke yi na komawa Jam’iyyar APC.
Ta ce Kwankwaso da ɗarikarsa ce ke da wannan shiri amma ba ita jam’iyyar NNPP ba.
Sakataren ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin a wani jawabi da ya fitar a garin Legas.
Kwankwaso wanda tsohon gwamnan Kano ne kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, a jawabin da ya yi a ranar Asabar ga magoya bayansa ya ce a shirye yake domin shiga jam’iyyar mai mulki ta APC.
Kwankwaso ya yi gargaɗin cewa shi da ɗarikarsa ta Kwankwasiyya ba za su lamunci a yi amfani da su wajen cin zaɓe sannan a yaɗa kwauransu ba daga baya.
A yayin da yake martani kan halin da ake ciki, Olaposi ya ce, abin da Kwankwaso ya faɗa a ƙarshe ya nuna cewa ya yarda shi da ɗarikarsa ba sa tare da NNPP.
“A ƙarshe, gaskiya ta yi halinta. Kenan duk wata tattauna da Kwankwaso zai yi ya kamata ya yi ne a matsayin shi kan kansa.
“Jam’iyyarmu za ta huta da tirjiyar da shi da ɗarikarsa ke yi bayan korarsu daga jam’iyyar saboda zargin cin dunduniyarta.
“NNPP ba ta da wani ƙullaci game da jam’iyya mai mulki, kuma idan lokacin zaɓen 2027 ya taho, kuma muka ga dacewar ƙulla haɗaka da APC, to za mu yanke wannan shawarar ne bakiɗaya.
“Amma a yanzu muna ƙoƙarin gyara gidanmu ne kafin zaɓe mai zuwa bayan rikice-rikice da shari’o’i da Kwankwaso da magoya bayansa suka jawo wa NNPP.”
A cewar, Olaposi, yarjejeniyar fahimtar juna da aka ƙulla tsakanin ɗarikar Kwankwasiyya da NNPP ya kare tun bayan zaɓen shugaban ƙasa a 2023.
“Rikicin ya samo asali a lokacin da a maimakon su bar jam’iyyar salin-alin, sai suke ƙoƙarin ƙwace jam’iyyar. Mun ƙagu mu gan su sun shiga wata jam’iyyar,” ya faɗa.
Sakataren Jam’iyyar na ƙasa, ya ce, Kwankwaso ba shi da sauran tasiri a siyasance domin dukkan magoya bayansa, da yawansu, sun shiga APC kafin wannan lokaci.
“Kwankwaso ba shi da jam’iyyam tasirinsa a siyasance ya kare bayan cin amanar NNPP wacce ta ba shi mafakar yi mata takara a lokacin da shigo jam’iyyar.”
“Duk ‘yan Nijeriya da suke tattaunawa da Kwankwaso da ɗarikarsa sun cewa suna yin magana ne da shi, amma ba da NNPP ba.
“Duk wata tattaunawa da sunan NNPP zai kasance marar amfani domin kuwa ya kasance korarre ne a wannan jam’iyya.”
Jigo a jam’iyyar ya koka kan jan ƙafa da ake samu daga INEC wajen wallafa sunayen sabbin shugabannin gudanarwa na jam’iyyar kamar yadda kotu ta ba da umarni inda ta amince da jagorancin Dr Agbo Major,” ya bayyana.
