Majalisar Wakilai ta amince da tiriliyan N54.990 a matsayin kasafin 2025

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar wakilai ta amince da kasafin kuɗin shekarar 2025, inda ta bar jimillar kuɗaɗen da za a kashe kan Naira tiriliyan 54.990.

A ranar 18 ga watan Disambar 2024 ne Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da ƙididdigar kasafin kuɗin a gaban zaman haɗin gwiwa na majalisar dokokin ƙasar, inda ya buƙaci amincewar da a yi ƙiyasin kashe kuɗaɗen farko na naira tiriliyan 49.74 na kasafin shekarar 2025.

Sai dai shugaban ya sake neman majalisar ta ƙara adadin kuɗaɗen daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2, saboda karin kuɗaɗen shiga da wasu manyan hukumomin gwamnati ke samu.

Majalisar wakilai ta amince da ƙudurin kasafin kuɗin a ranar Alhamis.

By ukarofi