Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kamfanin Sadarwa na MTN a Nijeriya ya sauya shirinsa na ƙarin kashi 200 cikin ɗari a 15GB.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ta hanyar asusunsa na ɗ a ranar Alhamis.
A farkon makon nan ne aka wayi gari da aarin kusan kashi 200 cikin ɗari, lamarin da ’yan aasar da dama suka yi Allah wadai da shi.
To sai dai cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a shafinsa na ɗ, ya ce yana sane da yadda masu amfani da layukansa suka nuna damuwa bayan da suka wayi gari kwatsam da ƙarin kusan kashi 200 na kuɗin data.
Kamfanin ya ce, zai iya bayar da dalilan da suka sa ya ɗauki matakin ƙarin, to sai dai ya ce in ma ya yi hakan ba zai gamsar ba.
”Saboda da haka mun karɓi laifinmu, mun yi kuskure, muna bayar da haƙuri kan hakan, a kuma yafe mana”, a cewar kamfanin.
ƙarin dai ya tayar da ƙura a Nijeriya, lamarin da ya sa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar, NLC ta buƙaci al’umma su ƙaurace wa amfani da layukan manyan kamfanonin wayar daga ƙarfe 11 na safe zuwa 2:00 na rana a kullum daga ranar Alhamis, 13 ga watan Fabarairu har zuwa 28 ga watan.
