Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta ƙaddamar da sabuwar rajistar mambobinta ta intanet da nufin samun cikakkun bayanan adadin mambobinta gabanin zaɓuƙan 2027 da ke tafe.
APCn ta bayar da kwangilar aikin ga wani kamfani mai zaman kansa mai Tunmef Global Limited, wanda zai jagoranci gudanar da aikin.
Yayin da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamarwar, shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya ce shirin na daga cikin dabarun jam’iyyar na amfani da fasahar zamani wajen tabbatar da matsayin jam’iyyar na wadda ta fi girma a ƙasar.
Ya kuma yaba wa shugaban ƙasar, Bola Tinubu bisa wannan dabara ta zamanantar da abubuwa.
”A yanzu komai na duniya ya koma na zamani, ba wanda yake amfani da hanyar gargajiya, kasuwanci na zamani, siyasa ta zamani, rayuwa ta zamani,” inji shi.
“Wannan fasaha za ta tabbatar da matsayinmu na cikakkiyar jam’iyya mai rajista, idan mun ce muna da mambobi miliyan 10, to ya kamata mu samu wannan adadi. Idan aka je zaɓe, idan muna da mutum miliyan guda a Legas alal misali, muna sa ran samun aƙalla ƙuri’a 500,000, saboda kowace jam’iyya na da irin nata manufofi.”
