Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Gwamnatin Jihar Kebbi ta soke takardun shaidar mallakar waɗansu magidanta gidaje da ke rukunin gidajen Sanata Atiku Bagudu Housing Estate da ke yankin ByePass a cikin garin Birnin Kebbi da suka kasa biyan kuɗaɗen gidajen.
Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Sakataren dindindin na ma’aikatar filaye da gidaje TPL Dr. Abubakar Ahmed.
Takardar ta buƙaci duk waɗanda abin ya shafa da su ɗauki abin da muhimmanci saboda gwamnatin jihar Kebbi ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakin da ya dace. Wannan ya shafi waɗanda ba su biya ba da kuma waɗanda suka soma biyan amma suka kasa cika kuɗaɗen.
Wannan umarni ya fara aiki nan take a matsayin wani yunƙuri na tabbatar da adalci da kuma kiyayewa da tsarin ingantaccen rarraba gidaje a jihar Kebbi.
