Makon Adabi: Ya kamata marubuta su dinga rubutu kan cigaban ƙasa – Sarkin Kano

Daga ZAHARADDEEN IBRAHIM KALLAH a Kano

A cikin makon da ya gabata ne dai Ƙungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA) reshen jihar Kano ta gudanar da Makon Adabi na Kano, wanda take gabatarwa shekara-shekara don yin bajakolin ayyukan fasaha tare da tattaunawa da marubuta da masu ruwa da tsaki a harkar rubutu, a yunƙurin ƙarfafar harkar adabi da matasa masu tasowa. 

A wannan shekara an yi wa taron take da Rubutu: Ginshiƙin Yayyata Al’adun Hausawa Ga Al’ummun Duniya, wanda aka gabatar a ɗakin karatu na Murtala Muhammad dake Kano tun daga ranar 2 zuwa 5 ga watan Nuwamba, 2022.

An fara taron ne da bikin buɗewa bisa jagorancin Farfesa Adamu Idirs Tanko, shugaban Jami’ar Baba-Ahmad dake Kano, wanda tsohon marubuci ne da aka rawa da shi wajen kafuwar ƙungiyar ANA Kano. Shugaban taron ya yi godiya da kasancewa a matsayin wanda zai jagoranci taron tare da fatan marubuta za su cigaba da bada gudunmawa a kan abin da aka jima ana ginawa. 

Farfesa Tanko ya ce a baya sun fuskanci ƙalubale ta yadda wasu mutane ba su karɓi ayyukansu ba, tare da yi musu gurguwar fahimta. Amma yanzu lokaci ya tabbatar da irin gudunmawar da aka bawa adabi, wanda ta buɗe ƙofofin nasarori. 

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda ya samu wakilcin Mai girma Ɗan Malikin Kano Alhaji Ahmad Umar, ya nuna farin cikinsa da Makon Adabi na Kano da ake gudanarwa a duk shekara.

Mai martaba Sarki ya yi kira ga marubuta su kalli wasu ɓangarori na rayuwar al’umma, musamman a wannan yanayi da ake ciki tare da yin rubutu a kai domin ilmantar da al’umma.

A cewar sa, yin haka zai kawo cigaban ƙasa, ba kawai abin da ya shafi soyayya ba kawai. Mai martaba sarkin ya yi fatan alheri ga mahalarta taron tare da fatan za a amfana daga abin za a tattauna. 

Kafin nan, a jawabin maraba, shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Najeriya, ANA reshen jihar Kano Arch. Tijjani Muhammad Musa ya yi farin cikin tare da godiya ga shugabanni da iyayen ƙasa da ɗimbin marubuta da suka halarci taron.

A jawabinsa ya ce ana gudanar da taron ne duk shekara, kuma a wannan shekara za a kwana huɗu ana gabatar da taron tare da sababbin shirye-shirye, inda za a rufe taron a ranar Asabar da liyar cin abin tare karrama waɗanda suka yi nasara a wasu gasanni na ɗalibai da marubuta. 

Farfesa Ibrahim Garba Satatima wanda ya kasance baƙo mai jawabi a taron ya yi waiwaye ne kan al’ummar Hausa da yadda ta shahara a Duniya tare da shiga loko da saƙo na duniya ta hanyar fatauci da neman ilmi a faɗin duniya, wanda hakan ya sa Hausa ta famtsama. 

Farfesan ya danganta Hausawa da rubutun ajami, wanda ke da daɗaɗɗen tarihi. Ya kuma danganta ajami da wasu al’ummu a duniya da suke amfani da shi a matsayin hanyar rubutunsu. 

Sai dai a jawabinsa ya nuna rashin samun cikakkiyar fahimta a kan ainahin rubutun da Hausawa suka ginu a kai tun kafin zuwa musulunci. Wannan ya sa masana ke tababa ko Hausawa na da rubutunsu, ko kuma sai da rubutun ajami ya bayyana.

Hakan ya sa shehun malami Farfesa Abdulƙadir Zangambo yin sharhi kan wasu rubuce-rubuce da aka gano a wasu keɓaɓɓun gurare da har yanzu babu wanda ya iya karantawa.

A cewar sa, tun da a tarihi babu wasu al’ummu da suka taɓa zama a guraren fashe Hausawa, hakan na iya zama hanyar rubutunsu ce ta dauri. A saboda haka ne ya yi kira da a cigaba da yin bincike a wannan ɓangare. 

Wannan bikin buɗewa na Makon Adabi na Kano ya samu halartar marubuta da masu ruwa da tsaki a rubutu da suka ƙunshi shugaban ɗakin karatu na Kano, Dr. Ibrahim A. Bichi da aka wakilce shi, da Farfesa Yusuf M. Adamu da Ado Ahmad Gidan Dabino (MON), da shugaban Hukumar Hisbah ta Kano da ya samu wakilci sai Drakta Maryam Ali Ali da Dakta Isa M. Inuwa. 

Hakazalika, akwai Farfesa Aliyu Kamal da Dakta Aminu I. Sagagi Malam Ismail Bala da Bala Anas Babinlata da Yahaya Dan Arewa da Hajiya Aisha Bilyaminu Usman, Ummasulaiman ‘Yan Awaki, sai kuma wanda ya jagoranci gabatar da taron Malam Nasiru Wada Khalil.

A tsawon kwanaki na Makon Adabi na Kano, an gudanar da shirye-shiryen adabi da suka jivanci tattaunawa da marubuta, gasar kacici-kacici a kan adabi ga ɗaliban makarantun sakandire da shirya gasannin rubutu da mahawara ga marubuta.

Akwai taron sanin makamar aiki, inda aka horar da marubuta yadda za su buga littafi da cinikinsa a kafofin sadarwa na zamani, da samun horo kan yadda za su ƙware a kan rubutun wasan kwaikwayo ko Fim da abin da ya shafi aikin fassara. 

Masana da marubuta da aka tattauna da su a tsawon kwanakin sun ƙunshi Aminu Sagagi da Ismail Bala da Dakta Nasir Salahudeen da Mal. Khalid Musa. Sannan akwai Nana Sule da Dr. Saka Aliyu da Hannatu Bilyaminu da Deborah Chiamaka Nwobodo.

Kamar yadda yake bisa al’adar marubuta a irin tarukansu, an gudanar da karance-karance da waƙe-waƙe don nishaɗantar da mahalarta taron tare da nuna baiwar da marubuta suke da ita wajen isar da saƙo cikin ƙwarewa iri-iri da take tafiya da zamani. 

Waɗanda suka jagoranci ire-iren waɗannan zama sun haɗa da Dr. Murtala M. Uba da Dr. Raliya Abdullahi Maijama’a da Zulkifl A G. Dakata da Khalid Imam. Akwai malamai irin su Da Ola Ifatimehim da Goni M. Mohammed da Dakta Danlami Gwammaja da Dakta Bala Muhammad.

An rufe taron ne da taron cin abincin dare tare da bada kambun yabo ga waɗanda suka yi nasara a gasar kacici-kacici tun daga ɗalibai zuwa marubuta. An yi wannan zama ne bisa jagorancin Ado Ahmad Gidan Dabino, tsohon shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA), reshen jihar Kano. 

Daga cikin waɗanda suka halarcin bikin cin abincin akwai fitattun marubuta irin su Nazir Adam Salihu da Nasir NID da Sadiya Garba da Bilkisu Yusuf Ali da Fauziyya D. Sulaiman da marubucin waqa Mal. Nasiru G. Ahmad ‘Yan Awaki da Hauwa Lawan Maiturare da Amina Yusuf Ali tare da Yaseer Kallah.  

Haka zalika, zaman ya samu halartar dukkanin gwarzayen gasar Hikayata ta BBC guda uku na wannan shekara, da kuma magabatansu na shekarun baya da suka haɗa da Maimuna Idris Beli da Rufaida Umar. 

An rufe taron da jawabin godiya daga sakataren ƙungiyar ANA Kano, Malam Mazhun Idris inda ya godewa shugabacin ANA Kano da jagororin kwamitoci da alƙalai da suka bada gudunmawa don tabbatuwar taron. Ya kuma godewa shugabancin ɗakin karatu na jihar Kano bisa jagoranci Dakta Ibrahim A. Bichi da shahin Amurka dake a ɗakin karatu ƙarƙashin Malam Nura Mudi. 

Zaharaddeen Ibrahim Kallah marubuci ne cikin harshen Turanci da Hausa, sannan tsohon shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA) reshen jihar Kano. Za a iya samun sa ta imel kamar haka: [email protected]