Garaɓasar ‘yan wasan Hausa a siyasar APC

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A makon da ya gabata na yi sharhi kan alaƙar mawaƙa, marubuta da ‘yan wasan Hausa a harkokin siyasa, inda na tavo tarihi da gwagwarmayar waɗannan ɓangarorin matasa masu aiki da fasaha a tsakanin ‘yan siyasa, da matakin da yanzu suka kai na rungumar harkokin siyasa gadan-gadan, don su ma a ci ribar dimukraɗiyya tare da su.

Bayan fitar wancan sharhi na makon jiya wata sabuwa ta bayyana, domin kuwa shigar waɗannan ‘yan wasan Hausa, mawaƙa da marubuta cikin siyasar 2023 ta sake kankama sosai. Yayin da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima, suka karɓi dandazon ‘yan wasan Hausa daga masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, don ba da gudunmawa a harkokin yaƙin neman zaɓe.

A ranar Talata da ta gabata, rahotanni daga Babban Ofishin Jam’iyyar APC na ƙasa ta bakin Kakakin Babban Daraktan yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar, wanda kuma shi ne Gwamnan Jihar Filato Simon Baƙo Lalong, ya bayyana cewa an ƙaddamar da tawagar ‘yan wasan Hausan ne domin cika alƙawarin da ɗan takarar shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi wa shugabannin ‘yan wasan waɗanda suka nuna masa goyon bayan su tare da gabatar da buƙatar su ta neman a basu damar shiga cikin yaƙin neman zavensa, a yayin ziyarar da ya kai Kano, a makonnin baya.

Sanarwar ta ce, ɗan takarar shugaban ƙasa ya yi musu alƙawarin ba su dama su shiga cikin tawagar yaƙin neman zaɓensa, kuma su yi amfani da ƙwarewar su da basirarsu wajen yaɗa saƙon ɗan takarar shugaban ƙasar ga al’ummar Nijeriya, a rubuce-rubucen su, waƙe waƙensu da finafinan da suke shiryawa, ta yadda za su ja ra’ayin jama’ar ƙasa su zaɓe shi.

Jerin sunayen tawagar ‘yan Kannywood ɗin da aka fitar ya nuna gamayyar ‘yan wasa da suka fito daga jihohin Arewa daban-daban, da suka haɗa da maza da mata, Musulmi da Kirista. Akwai shugabanni, daraktocin da iyayen tafiyar ‘yan wasa, da dattijan ‘yan wasa har mutum 54, ban da sauran mambobi aƙalla 50 da aka shigar da sunayensu, ban da waɗanda aka ce za a fitar a matakin jihohi.

Kusan za a iya cewa, ɗungurungum ɗin ‘yan wasan ne, ta babban mahaukaci, suka shiga wannan gangami da ake yi wa kallon za a sha romo da yawa a cikinsa. Ganin yadda ‘yan wasa maza da mata ke rige-rigen shiga cikin kwamitocin da aka ware kuma ake ganin da su ne za a gudanar da wannan babban aiki na yaƙin neman zaɓe, a matakin ƙasa da na jihohi. 

Masu hikimar magana na cewa, biri ya yi kama da mutum. Tururuwar da ake yi da sha’awar da kowa ke nunawa alama ce da ke kara tabbatar da hasashen da na yi na wancan makon cewa, shigar dandazon ‘yan fim a wannan tafiyar na nuna irin halin ƙuncin da ‘yan fim ke ciki na rashin samun tallafi da goyon bayan gwamnati da ‘yan siyasa ne ga cigaban harkokinsu.

Kuma ba su kaɗai ba, har ma da marubutan littattafan adabi da mawaƙa, da suka ce sun daɗe suna bautawa ‘yan siyasa, amma babu wata moriya ta a zo a gani da suka samu, sai yanzu da suka gano bakin zaren. 

Mai magana da yawun tawagar ‘yan Kannywood a takarar Tinubu, ɗan jarida ne marubuci, Nasir S. Gwangwazo, ya shaida min cewa, wannan tafiya ita ce mafita ga ‘yan fim, domin kuwa idan ba su shiga an tafi da su ba, za su yi asarar damarmaki da yawa. 

Ya nuna cewa, dole ce ta sa ‘yan fim ɗin Hausa da mawaƙa shiga harkar siyasa ganin irin yadda a shekarun baya aka riƙa tauye musu haƙƙi da zaluntar su ta fuskar shari’a, saboda wasu finafinai da suka shirya ko wasu waƙoƙi da suka fitar. Saboda a wani ɓangaren a na yi musu kallon ‘yan adawa ko marasa gata.

Amma shigar da wasunsu suka fara yi cikin siyasa, da ravar gwamnati mai ci ya sa an samu sauƙin abubuwa, ta yadda har aka ɗauki wani daga cikinsu yana shugabantar Hukumar Tace Finafinai, Ɗab’i da sauran ayyukan fasaha, wato Isma’il Afakallah, wanda a yanzu ma haka cikin wannan tafiya shi ne Mataimakin Daraktan tawagar yaƙin neman zaben Tinubu ƙarƙashin shugabancin Abdul Amart Mai Kwashewa. Kuma an samu sauyi daga abubuwan da suka faru a baya, na ɗauri da cin zarafin ‘yan fim da mawaƙa. 

A cewar Gwangwazo, idan har wannan ɗan takara na APC, Bola Ahmed Tinubu, ya samu nasarar zama Shugaban Ƙasa, babu shakka masana’antar Kannywood za ta amfana sosai. Suna sa ran shigar wasu daga cikinsu shiga cikin sabuwar gwamnati, da kuma samar wa masana’antar jari da shigar gwamnati cikin harkar, don a bunƙasa ta. Da kuma samar da tsare-tsare na zamani da za su ƙara inganta harkokin wasanni da rayuwar su kansu ‘yan wasan ta yadda za a sake musu mara, kuma a ba su dukkan goyon bayan da suke nema ƙarƙashin tsarin doka. 

Sai dai kuma yaya makomar sauran ‘yan fim ko mawaƙa da ba su da ra’ayin Jam’iyyar APC ko shiga siyasa, za a sha romon dimukuraɗiyyar babu su kenan? Nasir Gwangwazo ya ce, duk ganimar da za a samo ta masana’antar Kannywood ce gabaɗaya, ba ta zallar waɗanda aka yi gwagwarmayar yaƙin neman zaɓe da su ba ne kaɗai ba. 

Sakataren tawagar ‘yan fim na ƙasa, Sani Mu’azu Jos, ya bayyana cewa, kowanne ɗan fim mai sha’awar siyasa na da ’yancin shiga cikin gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyarsa, ba dole sai kowa ya shiga APC ba. Tun da duk inda aka samu nasara za a haɗu ne a yi aiki don cigaban Kannywood baki ɗaya. 

Ya ƙara da cewa, ‘yan fim sun shiga siyasa ne ba don kwaɗayin mulki ba, ko dukiya ba, sai don ƙwato haƙƙin sauran ‘yan fim da mawaƙa da kare mutuncin masana’antar Kannywood da kuma nema mata duk wata dama da za ta kai harkar fim ga gaci. 

Sai dai duk da uzurin da wakilan Kannywood ɗin ke bayarwa, wasu na ganin ba a yi daidai ba. Saboda a nasu ƙorafin bai kamata a shiga wannan tawagar yaƙin neman zaɓe da sunan Kannywood ba, domin sana’a ce ta mutane daban-daban, masu bambancin ra’ayin siyasa.

Darakta Auwal Y. Abdullahi, Mataimakin Shugaban MOPPAN a Jihar Filato na ganin kamata ya yi su fitar da wani suna na daban, kamar misalin yadda ƙungiyar haɗin gwiwar ‘yan fim da mawaƙa, magoya bayan Gwamnan Jihar Kogi, wato Yahaya Bello Network (YBN) ta Abdul Amart Mai Kwashewa, da ta ɓangaren Dauda Kahutu Rarara ta 13-13 suka yi. 

Ya ce, duk waɗannan ƙungiyoyi ne na ‘yan fim da mawaƙa da suke masana’antar Kannywood, amma ba su tsunduma siyasa da sunan Kannywood ba. Don haka abin da ya kamata su waɗanda suka shiga wannan tawaga ta Tinubu su yi, shi ne su tuntuvi ‘ya’yan ƙungiyar kafin amfani da sunan masana’antar wajen bayyana goyon bayansu ga wata jam’iyyar siyasa ko wani ɗan takara baya ba. Wannan shi ne babban kuskuren da ya ke ganin ‘yan wannan tawaga ta ‘yan wasa sun yi, saboda saurin ɗaukar matakin da suka yi kafin tuntuvar ‘yan ƙungiya da neman shawara. 

Darakta Auwal na fargabar yadda nan gaba makomar masana’antar Kannywood za ta kasance idan Jam’iyyar da suka marawa baya ta APC ta faɗi zaɓe, yaya gwamnatin da ta hau shugabanci za ta mutunta masana’antar?

Sai dai Kakakin tawagar Nasiru S. Gwangwazo ya ba shi amsa da cewa, kowanne ɗan Kannywood da ke goyon bayan kowacce jam’iyyar siyasa ya sa a ransa cewa, yana wannan siyasa ne ba kawai don cin moriyar kansa ba, yana so ne ya shigar da buƙatun wannan masana’anta, don ya za ma cikin manufofin sabuwar gwamnatin da za a kafa. Da kuma buɗewa Kannywood ƙarin ƙofofi don bunƙasar sana’ar fim, waƙoƙi da rubuce-rubucen adabin Hausa. 

Sannan kamar yadda wasu daga cikin ‘yan Kannywood ɗin ke kokawa, lallai ne a yi ƙoƙari a ga an tafi da kowanne ɓangare daga cikin turaku uku na wannan masana’anta, wato marubuta, mawaqa da ‘yan wasa. A kuma yi ƙoƙarin zaƙulo ‘yan wasa na sauran jihohi, da waɗanda suka daɗe suna ba da gudunmawa daga maza da mata, dattijai da matasa.

Saboda kada a cigaba da samun ƙorafe-ƙorafe kamar yadda a yanzu aka fara gani, a na kukan an manta da wasu da suka daɗe su na ba da gudunmawa, an zaɓi wasu da ake ganin masu baki ne ko tsagera, da za su iya yin rashin mutunci, idan an musu ba daidai ba.