Kamfanoni fiye da 5,600 sun halarci bikin CHTF karo na 24

Daga CMG HAUSA

An buɗe bikin baje kolin manyan na’urorin zamani na duniya na Sin karo na 24 a Shenzhen jiya Talata.

Faɗin yankin bikin da za a shafe kwanaki 5 ana gudanarwa ya kai sama da muraba’in mita dubu 300, wanda ya ja hankalin masu baje koli fiye da 5600 daga ƙasashe da yankuna 41 da kayayyaki fiye da 8600.

Jigon bikin shi ne “Gyare-gyare a fannin kimiyya da fasaha sun inganta ƙirƙire-ƙirƙire, kirkire-kirkiren kimiya sun ingiza bunƙasuwa ”.

A yayin bikin, a rumfar da ma’aikatar cinikayyar Sin ta kafa musamman, an nuna nasarorin da ƙasar Sin ta samu, wajen gina tsarin tattalin arziki mai salon buɗe ƙofa, da samar da sabbin damammaki a haɗin gwiwar tattalin arzikin ƙasa da ƙasa, da yin takara ta hanyar yin gyare-gyare da inganta cinikayyar ƙetare.

Baje kolin na musamman na ƙasar Sin, ya ƙunshi dandalin Intanet na abubuwa, da fasagar 5G “Smart+” da ragowar fasahohi da nasarorin masu nasaba.

Ma’aikatar aikin gona da raya yankunan karkara ta ƙasar Sin, ta mayar da hankali wajen nuna nasarorin da aka cimma a ɓangaren kimiya da fasaha da fasahar aikin gona ba tare da gurbata muhalli ba.

Bikin na bana ya shirya baje kolin nasarorin da aka cimma a fannin fasahohin zamani na tsimin ruwa a karon farko, da shirya taron ƙirƙira hanyoyin tsimin ruwana ƙasar Sin a karo na farko.

Mai fassara: Safiyah Ma