Ƙasar Sin ba ta taɓa mantawa da aminanta ƙasashen Afirka ba

Daga IBRAHIM YAYA

Yayin da shugabannin ƙasashe mambobin ƙungiyar G20 ke can suna tattauna batutuwa dake jan hankalin duniya, kamar farfaɗowar tattalin arzikin duniya da inganta tsarin kiwon lafiya da batun sauyin yanayi da sauya akala zuwa ga amfani da na’urori na zamani, har ma da batun samar da isasshen abinci da makamashi da makamantansu, a taron ƙungiyar dake zama na 17 a tsibirin Bali dake ƙasar Indonesia.

Ƙungiyar G20 da aka kafa a shekarar 1999, ta zama wani muhimmin dandalin haɗin gwiwar ƙasashen duniya a fannin raya hada-hadar kuɗaɗe da tattalin arziki.

Kuma yanzu haka tana da ƙasashe mambobi 19 gami da ƙungiyar tarayyar Turai (EU).

A yayin da ɓangarorin ƙasa da ƙasa ke fatan ganin manyan ƙasashe masu sukuni za su ƙarfafa tsarin gudanarwa a fannin manufofin cuɗanyar ɓangarori daban-daban da kara buɗe ƙofa da tafiya tare da kowa da hadin gwiwar moriyar bai ɗaya, shi kuwa shugaba Xi Jinping na ƙasar Sin, ya bayyana goyon bayan shigar da ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ne a cikin ƙungiyar ta G20.

Wannan batu da shugaba Xi ya gabatar ya ƙara tabbatar da cewa, ƙasashen Sin da Afirka sun zama abin da Malam Bahaushe ke cewa, “’yan uwa rabin jiki”.

Kuma a duk lokacin da ɓangaren Sin ya ga abin da zai shafi moriyar ƙasashen Afirka musamman ƙasashen masu tasowa, ya kan yi ƙoƙarin nusar da duniya buƙatar kare muradunsu tare da mara musu baya, wajen ganin an cimma burin da ake fata, matakin dake ƙara jaddada sahihancin haɗin gwiwar sassan biyu.

Sanin kowa ne cewa, ƙasashen duniya musamman masu tasowa, wanda ƙasashen Afirka ke ciki, suna fuskantar ƙalubale na koma bayan tattalin arziki.

Wannan ne ma ya sa shugaba Xi ya gabatar da shawarar kafa dangantakar abokantakar neman farfaɗo da tattalin arziki da dora muhimmanci ga aikin neman ci gaba da raya al’umma.

Saɓanin yadda wasu ƙasashe ke neman kafa kansa ba tare da la’akari da ragowar ƙasashe ba, wai kowa ya kar kifi gorarsa.

Shi kuwa shugaba Xi, cewa ya yi, ya dace irin waɗannan ƙasashe su taimakawa sauran ƙasashe, da ba su karin damammakin da suke buƙata.

Wato ka so wa dan uwanka, abin da kake so a kanka.

Baya ga kayayyakin more rayuwa da ƙasashen Afirka suka amfana da su ƙarƙashin haɗin gwiwar sassan biyu, wato Sin da Afirka.

Daga lokaci zuwa lokaci ko dai a taruka ko dandalolin ƙasa da ƙasa, ɓangaren Sin kan yi ƙoƙarin kare muradun ƙasashe masu tasowa baki ɗaya.

Ƙasar Sin ba ta taba mantawa da aminanta ƙasashe Afirka ba.

Abin da ke ƙara tabbatar da sahihancin alaƙar sassan biyu.