Sin za ta ci gaba da haɗa hannu da mambobin G20 game da tsarin tattalin arziki na zamani

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya ce a shirye Sin take, ta ci gaba da haɗa gwiwa da ƙasashe mambobin ƙungiyar G20, wajen gina tsarin tattalin azikin duniya na zamani, wanda zai kasance dunƙulalle, bisa daidaito da haɗin gwiwa da moriyar juna da ci gaba na bai ɗaya da kowa zai mora.

Xi Jinping ya bayyana haka ne a yau Laraba, yayin da yake jawabi ga taron ƙolin G20 karo na 17 a tsibirin Bali, na ƙasar Indonesia.

Da ake tattaunawa game da komawa amfani da fasahohin zamani, shugaba Xi ya ce faɗaɗa tattalin arziki irin na zamani da hanzarta komawa amfani da fasahohin zamani, sun zamo muhimman batutuwan dake tasiri kan tsarin tattalin arzikin duniya.

Yayin taron G20 da aka yi a Hangzhou a shekarar 2016, a karon farko, ƙasar Sin ta sanya batun tattalin arziki na zamani cikin ajandar taron, inda ta lashi takobin ƙirƙiro hanyoyin samun ci gaba tare da lalubo damarmakin ci gaba dake akwai.

Shugaban na Sin ya ce kamata ya yi a bayar da fifiko ga samun ci gaba, inda ya ce wajibi ne a cike gibin fasahohin zamani dake akwai, haka kuma ƙirƙire-ƙirƙire ya zama jigon ingiza ci gaba, bayan shawo kan annobar COVID-19.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha