Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Marigayi Alhaji Abbas Sunusi Galadiman Kano wanda ya kwanta dama a makon da ya gabata, yana da shekara 97 a duniya, kuma wanda ya fara shiga sha’anin mulki tun yana ɗan shekara 13, kamar yadda makusanta masoya suka tabbatar da wannan a rahotanni daban-daban da suka fito bayan rasuwar Galadiman Kano.
Bayan rasuwarsa kuma ya na da ‘ya’ya 37 cikin 40 da Allah ya azurta Marigayi Galadiman Kano, ya yi suna sosai da daɗewa akan muƙamin Wamban Kano wanda daga baya ya zama Gaadiman Kano bayan muƙamai daban-daban da ya riƙe a masarautar Kano a rayuwarsa.
Sai dai kuma bayan rasuwarsa daga cikin ɗimbin malamai da suka bayyana ra’ayoyinsu a rahotanni daban-daban sun bayyana Galadiman Kano a matsayin mai haƙuri da kawai ci da sanin ya kamata, kaɗan daga cikinsu akwai s’Sheikh Kamalu Inuwa, Sarkin Malaman Galadiman Kano babban limamin masallacin Juma’a na Hidaya da ke Kundila wandila Gandun Albasa Kano, ya bayyana cewa galadinman kano marigayi Alhaji Abbas Sunusi shi da marigayi galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim sun yi sarauta da ta taimaki mutanan kano ta fuskoki da dama ko da kuwa jama’a ba su sani ba amma mu mun san haka saboda haƙuri da juriya da Allah ya ba su a zamanin rayuwarsu, kamar yadda sheikh Ibrahim Khalil shi ma ya bayyana haƙurin haka sauran Malamai irin su Farfesa Abdullah Sale Pakistan Wanda ya samu wakilcin Sheikh Bichi maitaimakinsa a ƙungiyar Izala ta ƙasa reshan jahar kano ya bayyana, Haka sauran malaman sun haɗa da malaman Tijjani Bala ƙalarawi, Malam Tasiu Abdurrahman Kofar Waika, da dai sauransu.
Haka su ma shugabannin Faruku Iya Sambo tsohon kwamishinan ilimi, Hon. Bala Gwagwarwa tsohon kwamishinan albarkatun ruwa na Kano, sai Hon. Ado Kibiya tsohon kwamishinan albarkatun gona, tsohon kwamishinan filaye na Jihar Kano Hon. Aminu Dabo, injiniya Bello sani Gwarzo Tsohon muƙaddashin shugaban raya kogunan da Haɗejia da Jama’are, wanda ya 11samu rakiyar Alhaji Abdullahi Madugu su ga ban Datasen Technologies da sauran ma’aikatan sa, sai kuma manyan ‘yan kasuwa irin ‘yan kasuwa Sabitu Yahaya Jifatu, Rabiu Abubakar Tumfafi Babban sakatatare a ƙungiyar kasuwar Dawanau Muhammad Uba Gurjiya, sai kuma kallabi tsakanin rauna Hajiya Namadi Bebeji mai bai wa gwamnan Kano shawara kan harkar al’amuran gyaran hali da sauransu.
A ƙarshe Alhaji Kabiru Abbas Sunusi babban ɗa ga marigayi galadiman kano da Alhaji Mu’awiya Sunusi ɗan Makwayon Kano, sai kuma Hajiya Amina Abbas Sunusi wacce akafi sani da Kilishi, Hajiya Yahanasu Abbas Sunusi duk kanin su, sun bayyana marigayi galadiman kano a matsayin uba kuma shugaba abun koyi wajan haƙuri jarumta da sanin ya kamata a matsayin abun da za’a ɗora a sauran rayuwarsu, da sauran ‘yan uwansu, da al’umma baki ɗaya.
