NRC ta karrama Shugaban NDC, Farfesa Ma’aji

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Kungiyar Mazauna Gidajen Na’ibawa da ke ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano wato Na’ibawa Residence Community (NRC) ta karrama shugaban hukumar NDC Farfesa Shehu Abdullahi Ma’aji, ta farfaɗo da raya jihohin arewa maso yamma, wanda su ka haɗa jihohi bakwai, ƙarƙashin shugabancin Farfesa Ma’aji shugaban hukumar na farko bayan ƙirƙiro wannan hukuma da Hon. DSP Sanata Barau I. Jibrin ya jagoranci neman kafata mai shelkwata a Kano.

NRC ƙarƙashin shugabancin Injiniya Murtala Alhaji Garba, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar NSE ta Injiniyoyi ta Nijeriya reshen Jihar Kano, ya ce sun karrama wannan bawan Allah ne a matsayinsa na maƙoci kuma ɗan uwa, wanda ake mu’amala ta yau da kullum tare, don haka ne su ka shirya wannan taro don a yi masa fatan alkairi da addu’a da fatan gamawa lafiya ta hanyar neman yadda Ubangiji ya yi masa jagorancin na samun nasara a wannan shugabanci da aka ɗora masa na wannan hukumar ta Northwest Deɓelopment Commission (NDC), wanda taro ya haɗa da malamai, dattawa, matasa, mata da sauransu domin neman addu’a, kowane mutum da ya halarci wannan taro da ma wanda bai halarta ba addu’ar alkairi ga Farfesa Ma’aji.

ɗaya daga cikin malamai da suka halarci wannan taron karramawa Dr. Abdullah Usman Gadon ƙaya, nasiha ya yi ga sabon shugaban na cewa ka da ya yarda ya rabu da masoyansa waɗanda za su ba shi shawara tagari, kuma ka da ya yarda ya manta da matsalolin da Arewa take ciki na matsalar tsaro, lafiya, ilimi, noma, rashin aikin yi, da sauran matsaloli da suka dabaibaiye arewa suka hana ta cigaba, wanda shi Farfesa Ma’aji yanzu shi ne babban wakilin shugaban ƙasa Tinubu a wannan yanki a wajen mu a cewar Dr. Abdullah Usman Gadon ƙaya a nasiharsa da fatan alkairinsa da addu’a ga shugaban NDC.

Shi ma a jawabinsa, Farfesa Ma’aji wanda ya samu rakiyar mai ɗakinsa Hajiya Ramatu Shehu Ma’aji da sauran makusanta, abokan aiki, masoya irin su Hon. Garko, da maƙota da sauransu, ya bayyana jin daɗi da godiyarsa ga Allah maɗaukacin Sarki kan wannan dama da ya samu ƙarƙashin jagorancin DSP Barau Jibrin, da karramawa da maƙota su ka shirya masa inda kuma ya bayyana cewa wannan shugabanci babban nawune akan sa wanda ya ke buƙatar addu’a da shawarwari ta gari daga waɗanda aka sani da ma waɗanda ba’a sani domin idan aka yi nasara to cigaban musulinci ne aka sin haka kuma abu ne da baza a so ba, kuma ya bayyana abubuwa guda bakwai da aka dorawa wannan hukuma na ganin an samu cigaba da tabbatar da maƙasu din kafata. Kaɗan daga ciki sun haɗa da tabbatar da tsaro, ilimi, lafiya, bunƙasa noma, samar da aikin yi ga matasa, inganta kasuwanci.

A ƙarshe ya yaba wa Injiniya Murtala Alhaji Garba shugaban NSE kuma shugaban NRC da sakataren ƙungiyar malaman Sani Tanko da sauran mambobin wannan ƙungiya kan shirya wannan taro mai ɗimbin tarihi da albarka a tsakanin al’ummar wannan unguwa, Kano, arewa, Nijeriya da baki ɗaya.

By ukarofi