Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Malaman addinin Musulunci daga mabambantan ƙungiyoyi da mabiya ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) sun yi kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa da gaskiya, tare da tabbatar da adalci kan kisan Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka da wasu ’yan bindiga da ake zargi suka yi.
Malaman sun bayyana wannan buƙata ne a wani taro da suka gudanar a Jihar Katsina, inda suka ce tabbatar da adalci ne kawai zai iya hana sake kai hare-hare da kashe malaman addini da masu wa’azi marasa laifi.
Taron, wanda aka shirya ƙarƙashin inuwar ƙuranic Belieɓers Harmony for Peace Initiatiɓe, ya kuma kasance wata dama ta tunawa da Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, wanda shi ne ya fara shirin gudanar da zaman addu’o’in, amma wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kashe shi kwanaki kaɗan kafin gudanar da taron.
An gudanar da taron mai taken “National Unity Gathering for Prayers, Peace and Unity”, inda ya haɗa mambobin ƙungiyar Islamic Moɓement of Nigeria, wadda aka fi sani da Shi’a, da ƙungiyoyin ƙadiriyya, Tijjaniyya da Ahlus Sunnah, tare da shugabannin Kiristoci daga sassa daban-daban na ƙasar.
Mahalarta taron sun bayyana cewa manufar shirin ita ce ƙarfafa haɗin kai tsakanin ’yan Nijeriya ba tare da la’akari da ƙabila ko bambancin addini ba.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban ƙungiyar CAN na Jihar Katsina, Rabaran Richard Shuaibu Danliti, ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki na inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da kuma ƙarfafa haɗin kan ƙasa.
Ya yaba wa mahalarta taron bisa halartar shirin da kuma tabbatar da gudanar da zaman addu’o’in duk da kisan wanda ya assasa shi.
“Mun yaba wa mabiya addinai daban-daban bisa yadda suka haɗa kai suka kuma tabbatar da nasarar gudanar da addu’o’in,” in ji shi.
Danliti ya tabbatar da cewa CAN za ta yi aiki da sakamakon taron, tare da ci gaba da ƙoƙarin inganta haɗin kai tsakanin ’yan Nijeriya da zaman lafiya a ƙasar.
Haka kuma, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su ci gaba da gudanar da addu’o’i domin ganin an gudanar da babban zaɓen 2027 cikin nasara da lumana.
A nasa ɓangaren, Shugaban ƙasa na ƙungiyar Islamic Movement of Nigeria, Sheikh Ibrahim Zakzaky, wanda Farfesa Abdullahi Yahaya ya wakilta, ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da yaɗa koyarwa da manufofin marigayi Masussuka, musamman yadda yake jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin ’yan Nijeriya.
.
