Mamakon ruwan sama ya yi sanadin ɗaiɗaita yara 470 da lalata gidaje 270 a Zariya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani mamakon ruwan sama da aka yi tsakanin ranakun Alhamis da Juma’a a Zariya, Jihar Kaduna, ya yi sanadiyyar ɗaiɗaita sama da yara guda 470 da lalata gidaje aƙalla 270 sakamakon mafi munin ambaliya tsawon a yankin.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Zariya, Alhaji Ahmad Muhammad Jaga ya jagoranci wata ziyara ta gani da ido da haɗin-gwiwar Ƙungiyar bada agaji ta Nigerian Red Cross Society da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), inda suke je unguwannin da iftila’in ya rutsa da su domin duba matakin ɓarnar da aka samu.

Daga cikin yankunan da suka ziyarta akwai Ƙofar Kuyanbana, Gangaren Mobil, Bayan Cinema a Tudun Wada, Magume, Bako Zuntu, da kuma Kamacha a Tukur Tukur, inda ambaliyar ta shafe gidaje, kayan abinci da na wutar lantarki da dai sauransu.

Al’umma sun bayyana halin firgici da suka samu kansu a ciki a lokacin da ruwa ya mamaye gidajensu, lamarin da ya tilasta musu ficewa neman mafaka a tsakiyar dare.

Tuni jami’an Red Cross reshen Zariya suka fara raba kayayyakin tallafi kamar abinci, barguna da kai ɗaukin gaggawa ga iyalan da suka ɗaiɗaice.

A sanarwar da kungiyar ta fitar, ta ce har yanzu akwai buƙatar kai kayayyakin jinƙai ga mutanen da iftila’in ya rutsa da su duba da yadda suke cikin mawuyacin hali.

By Babaji