
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni daga ƙasar Burkina Faso sun bayyana cewa, Gwamnatin ƙasar ta sanar da ɗauke kuɗin biza akan dukkan ƴan Afirka da ke son shiga ƙasar domin inganta haɗin kai a shiyyar da bunƙasa walwalar al’umma.
Ministan Tsaron ƙasar, Mahamadou Sana ya bayyana haka a wani saƙo ranar Alhamis, bayan wani zama da shugaban mulkin sojin ƙasar, Kyaftin Ibrahim Traoré.
Ya ce, daga yanzu duk wani ɗan Afirka da ke da muradin zuwa Burkina Faso, an sauke masa kuɗin biza.
Saidai duk da ci-gaban, matafiya za su riƙa cike fom na neman biza kafin a tabbatar da su, kamar yadda ya ƙara faɗa acikin saƙon.
A cewar BBC, sabon tsarin ya shigar da Burkina Faso sahun ƙasashen da ke amfanin da irinsa kamar su Rwanda, Kenya da Ghana, waɗanda su ma a ƴan shekarun nan suka samar da rangwame ga ƴan Afirka da ke zuwa cikinsu domin walwala ko wasu harkoki.
A shekarar 2022, Shugaba Traoré ya karɓe mulki a Burkina Faso bayan wani juyin mulki, inda ya ke fafutukar samar da haɗin kai mai ƙarfi a tsakanin ƙasashen Afirka, wanda a wasu lokutan ya kan soki mulkin Turawan Yamma da ababen da Turawan mulkin mallaka suka dasa a ƙasashen Nahiyar, inda a gefe guda kuma yake ƙoƙarin ƙulla ƙawance da Rasha.
