Manchester United ta maye gurbin Carrick da Pochettino a matsayin kocinta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar ƙwallon ƙafar Manchester United ta ƙasar Ingila, ta sallamin kociyan ‘yan wasanta Michael Carrick, biyo bayan nazari da hukumar gudanarwarta ta yi kan halin tsaka-mai-wuya da United ɗin ta samu kanta a ciki a farkon wannan kaka ta 2026/27.

An yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, wanda ya kawo ƙarshe zaman Carrick a matsayin kocin ƙungiyar a lokacin da aka tattauna tsakanin shugaba Omar Berrada, daraktan ƙwallon ƙafa Jason Wilcox da Sir Jim Ratcliffe, wanda ɗaya ne daga cikin masu ƙungiyar na marasa rinjaye.

Wannan ya biyo bayan tsawon makonni ana raɗe-raɗi kan makomar Carrick a United, inda hukumar gudanarwar ta riƙa tattaunawa kan halin rashin nasarar da take fuskanta, wanda ya kai ga ta tsinci kanta a halin fita daga gasar Premier League, inda take mataki na 18 da ke nuna cewa akwai tazarar maki 19 tsakaninta da Arsenal, wadda ke ta ɗaya a teburi bayan wasanni 10.

Tuni dai tsohon mai horar da ‘yan wasan Tottenham da Chelsea, Mauricio Pochettino ya amince da karɓar aikin horar da ‘yan wasan United. Ɗan Ajantinan, wanda shi ne kocin Amurka na yanzu, ya shirya tsaf domin dawo wa Premier League da karɓar aiki a Old Trafford.

Ana sa ran United za ta biya Amurka Fam miliyan 7 a matsayin kuɗin barinsa aikin jagoran ‘yan wasan nata. Za a aiwatar da haka ne ganin cewa ya rattaɓa hannu a sabon kwantaragin da zai sa ya cigaba da riƙe ƙasar har zuwa lokacin gasar Kofin Duniya ta 2030. Sannan, zai jagoranci Amurka a wasanta da Haiti na ranar 14 ga Nuwamba kana daga bisani ya karɓi ragamar horar da ‘yan United.

A watan Junairun 2026 ne dai aka naɗa Carrick a matsayin kociyan United bayan ƙungiyar ta sallami Ruben Amorim kan rashin taɓuka abin a-zo-a-gani. Matakin na yanzu ya nuna cewa ƙungiyar ta naɗa koci na 13 cikin shekaru 13 tun bayan barin Sir Alex Ferguson muƙamin a shekarar 2013, wanda ya shafe tsawon shekaru 27 yana jagorantar ƙungiyar, inda a lokacin ne ya taimaka mata lashe Champions League guda biyu, Premier League 13, FA Cup 5 da dai sauransu.

By Babaji

Leave a Reply