Manyan jiga-jigan siyasar Gawuna na shirin komawa APC a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu manyan jiga-jigan siyasa masu biyayya ga tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, na shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar NDC zuwa jam’iyyar APC.

Hakan ya biyo bayan wata ziyarar haɗin kai da tawagar ’yan siyasar ta kai wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da Mataimakinsa, Murtala Sule Garo.

Mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Tawagar, wadda wani na hannun daman Gawuna, Hon. Muhammad Badaru Umar, ya jagoranta, ta haɗa da Mataimakin Shugaban NDC na Jihar Kano, Hon. Ali Datti Yako; Hon. Mansur Isa Gawuna; da Hon. Uba Tanko Mijinyawa, wanda aka fi sani da Uba Danzainab.

Sauran mambobin tawagar sun haɗa da Hon. Aminu Umar Faruk, Hon. Sani Jibrin, Hon. Salisu Muhammad, Hon. Musa Sani Indabo, Hon. Muhammad Kabir Bala, Hon. Hassan Abba Abdullahi da Comrade Abdurrahman Muhammad.

Da yake magana yayin ziyarar, Muhammad Badaru Umar ya ce sun yanke shawarar ganawa da Gwamna Yusuf da Mataimakinsa ne sakamakon kishinsu da ci gaban Jihar Kano.

Ya bayyana cewa ziyarar wani ɓangare ne na shawarwari da tuntubar juna da suke gudanarwa, tare da ƙoƙarinsu na bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.

Shi ma Hon. Ali Datti Yako ya ce al’ummar Kano sun san irin ƙoƙarin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi wajen sauya fasalin jihar.

“Duk duniya ta san cewa Gwamna Yusuf yana aiki tuƙuru domin sauya fasalin Jihar Kano,” inji shi.

Tawagar ta kuma bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamna Yusuf da Mataimakinsa, tare da jaddada aniyarta ta ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ci gaba da bunƙasar Jihar Kano.

Ana kallon wannan ci gaba a matsayin wani sabon sauyin siyasa a Jihar Kano gabanin babban zaɓen shekarar 2027, yayin da ake sa ran komawar wasu daga cikin manyan ’yan siyasar da ke tare da Gawuna zuwa APC za ta ƙara ƙarfafa jam’iyyar a jihar.

By ukarofi