Yadda ƙungiyar mafarautan namun daji ta Kudancin Nijeriya ta fara tattaunawar haɗin kai a Ogun

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

ƙungiyar Mafarautan Namun Daji ta Jihohin Kudu maso Yammacin Nijeriya ta gudanar da wani taro na musamman da nufin ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin mambobinta.

An gudanar da taron ne a ranar Juma’a da ta gabata a garin Ogere da ke Jihar Ogun, inda wasu daga cikin mambobin ƙungiyar daga sassa daban-daban na jihar suka halarta.

A yayin taron, shugabannin ƙungiyar da mambobinta sun gabatar da jawabai tare da bayar da shawarwari kan hanyoyin da za a bi domin ƙara bunƙasa ƙungiyar, da kuma ɗaukaka martabarta a faɗin Nijeriya.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Alhaji Bole, ɗan asalin Jihar Kano wanda yake riƙe da wani muƙami na shugabanci a reshen ƙungiyar da ke Ogere, da Alhaji Kabiru Cabi, shi ma ɗan asalin Jihar Kano. Haka kuma, taron ya samu halartar ɗan autan mafarautan Ogere, Alhaji Dan Jabba Kano, da sauran mambobin ƙungiyar.

Da yake bayani kan dalilin gudanar da taron, Shugaban ƙungiyar Mafarautan Namun Daji ta Jihohin Kudu maso Yammacin Nijeriya, Alhaji Kabiru Ori Ogere, ya ce an shirya taron ne domin ƙara ƙarfafa haɗin kan mambobin ƙungiyar da kuma samar da damar tattaunawa kan hanyoyin da za su taimaka wajen ci gaban ƙungiyar.

Ya ce, taron ya kuma kasance wata dama ta tattauna matsalolin da ƙungiyar ke fuskanta a wasu daga cikin jihohin Kudu maso Yammacin Nijeriya, tare da nemo hanyoyin magance su.

Alhaji Kabiru Ori Ogere ya ce ɗaya daga cikin manyan walubalen da ƙungiyar ke fuskanta shi ne yadda wasu jami’an tsaro da ma’aikatan wasu jihohi ke kama mambobinta a lokacin da suke gudanar da ayyukan farauta a daji, bisa zargin cewa ’yan fashi ne ko kuma ’yan ta’adda.

A cewarsa, irin wannan zargi ba shi da tushe, domin aikin mambobin ƙungiyar na farauta ne, kuma ba su da wata alaƙa da aikata laifuka ko ayyukan ta’addanci.

Ya ce a lokuta da dama, idan mafarautan suka shiga dazuzzukan da ake zargin ’yan fashi da makami suna fakewa, ’yan fashin kan gudu su bar dajin saboda tsoron mafarautan, yana mai cewa wannan ma ya nuna cewa babu wata alaƙa ko haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar da masu aikata laifuka.

Shugaban ya jaddada cewa ƙungiyar Mafarautan Namun Daji ba ta da wata alaƙa da fashi da makami ko ta’addanci, yana mai cewa ba daidai ba ne a ɗauki mambobinta a matsayin masu aikata laifuka saboda kawai suna gudanar da farauta a daji.

Ya kuma bayyana cewa ƙungiyar tana da cikakkiyar rajista, sannan ya ce mambobinta ba sa kallon farauta a matsayin sana’ar dogaro da kai, illa dai suna gudanar da ita ne domin kiyaye da kuma raya al’adun gargajiya da suka gada daga kakanninsu.

Alhaji Kabiru Ori Ogere ya yi kira ga gwamnatocin jihohin Kudu maso Yammacin Nijeriya da su riƙa gudanar da cikakken bincike kafin kama ko tsare mambobin ƙungiyar, domin kauce wa yin hukunci bisa zato ko rashin cikakken bayani.

Ya ce yin hakan zai taimaka wajen kare mutuncin mafarautan da ke gudanar da ayyukansu bisa ƙa’ida, tare da ƙarfafa kyakkyawar alaƙa tsakanin ƙungiyar da hukumomin gwamnati da jami’an tsaro.

By ukarofi