Daga MUHAMMADU MUJITABA a KANO
Kungiyar Ma’aikatan Makarantun Sakandare ta Jihar Kano (ASUSS), ƙarƙashin jagorancin Kwamared Abdu Usman Yalo, ta yaba wa hukumar Makarantar ’Yan Mata ta Mairo Tijjani Government Science and Technical College Kano (MTGSCK), ƙarƙashin shugabancin Hajiya Rabi Jafar Baba, kan yadda ta shirya taron karrama ɗalibai, malamai da shugabannin makarantu da suka nuna ƙwazo da bayar da gagarumar gudummawa wajen bunƙasa ilimi da sauran fannoni na rayuwar al’umma.
An bayyana hakan ne yayin wani taron raba kyaututtuka da makarantar MTGSCK ta shirya a Kano a makon da ya gabata.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban ASUSS na Jihar Kano, Kwamared Abdu Usman Yalo, ya ce irin wannan taro na da muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa gwiwar ɗalibai, malamai da shugabanni domin su ƙara himma wajen inganta harkokin ilimi.
Ya ce karrama waɗanda suka yi fice ba wai kawai wata hanya ce ta yaba musu da ƙoƙarinsu ba, har ma tana ƙarfafa wasu da su yi koyi da kyawawan halayensu da gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban al’umma.
Kwamared Yalo ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, kan irin ƙoƙarin da yake yi wajen bunƙasa ilimi a matakai daban-daban, yana mai cewa biyan albashin ma’aikata a kan lokaci, ciki har da ranar 25 ga kowane wata ko da ta kama Asabar ko Lahadi, na daga cikin abubuwan da gwamnati ta yi na inganta jin daɗin ma’aikata.
Ya ƙara da cewa biyan wasu haƙƙoƙin ma’aikata, ciki har da fansho da garatuti da sauran su, na daga cikin dalilan da suka sa ASUSS ke mara wa gwamnatin jihar baya, yana mai cewa ƙungiyar za ta ci gaba da kasancewa tare da gwamnan har zuwa shekarar 2027, da yardar Allah.
Shi ma Babban Sakataren Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (STSB), Farfesa Tahiru Saleh Muhammad, ya bayyana cewa zuwan gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya haifar da ƙarin makarantun kimiyya da fasaha a jihar.
Farfesa Tahiru ya ce wasu daga cikin sabbin makarantun za su fara karatu nan ba da jimawa ba, yana mai cewa hakan zai ƙara bunƙasa fannin ilimin kimiyya da fasaha tare da samar da ƙarin damar samun ilimi ga ɗaliban jihar.
Ya ce gwamnatin Kano ta kawo sauye-sauye masu muhimmanci a fannin ilimi, musamman a ɓangaren kimiyya da fasaha, domin tabbatar da cewa matasa sun samu ilimin da zai taimaka musu wajen fuskantar ƙalubalen rayuwa da kuma bayar da gudummawa ga ci gaban jihar.
A nasa ɓangaren, ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban makarantar, Alhaji Yusuf Ali Zaki, wanda ya shahara wajen tallafa wa MTGSCK, ya jaddada muhimmancin bayar da gudunmawa wajen bunƙasa ilimi.
Ya ce ilimi na kowa ne, don haka ya zama wajibi ga masu hali da sauran masu ruwa da tsaki su tallafa wa makarantu da ɗaliban da ke buƙatar taimako domin tabbatar da ci gaban ilimi a kowane lokaci.
Alhaji Zaki ya bayyana cewa ɗiyarsa, wadda ta kammala karatunta a makarantar, ita ce da kanta ta nemi a mayar da ita makarantar gwamnati domin ta ga yadda ’yan uwanta ɗalibai ke gudanar da rayuwarsu a makarantar gwamnati, tare da samun damar ƙara wayewa da hulɗa da sauran ɗalibai.
Ya ce tun bayan dawowarta makarantar, lamarin ya zama alheri ba gare shi kaɗai ba, har ma ga wasu ɗalibai, domin ɗiyarsa kan sanar da shi buƙatun ɗaliban da suke buƙatar tallafi.
Alhaji Zaki ya yi alƙawarin ci gaba da tallafa wa makarantar MTGSCK gwargwadon ƙarfinsa har ƙarshen rayuwarsa, da izinin Allah.
A ƙarshe, Alhaji Habibu Abdullahi Dan Amar ɗan Tofa, wanda ya wakilci Makaman Bichi, Alhaji Isyaku Umar Tofa, na daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron, tare da wasu manyan baki ciki har da Hakimin Gari na Kano, Malam Khalacan Kano.
Manyan baƙin sun bayyana gamsuwarsu da yadda aka gudanar da taron, tare da yaba wa hukumar makarantar kan ƙoƙarin da take yi wajen ƙarfafa gwiwar ɗalibai da malamai.
Shugabar makarantar, Hajiya Rabi Jafar Baba, ita ma ta bayyana shugaban Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (STSB) a matsayin wanda ke riƙe da amanar Gwamna Abba Kabir Yusuf da gaskiya da riƙon amana.
Ta bayyana hakan ne ta bakin mataimakiyar shugabar makarantar, Aishatu Rabi’u Ishaƙ, bayan kammala taron a wannan rana.
