Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (FWF) ta rubuta wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Majalisar Dokoki, tana neman a gaggauta sake duba albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya tare da ƙara mafi ƙarancin albashi daga Naira 70,000 zuwa Naira 300,000.
ƙungiyar ta kuma nemi a ƙayyade albashin ma’aikatan mataki na 17 zuwa Naira miliyan 1.5 a wata, tana mai cewa tsarin albashin da ake amfani da shi a yanzu bai sake dacewa da tsadar rayuwa da ƙalubalen tattalin arzikin da ma’aikatan gwamnatin tarayya ke fuskanta ba.
Wasiƙar, mai ɗauke da kwanan wata 2 ga Satumba 2026, wadda Mai Gudanar da Ayyukan ƙasa na FWF, Andrew Emelieze, da Babban Sakataren ƙungiyar, Ogundele Ayodele, suka sanya wa hannu, an aika ta ne zuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai ta hannun Magatakardan Majalisar Dokoki.
An kuma aika kwafin wasiƙar zuwa ga Shugaban ƙasa Tinubu, Babban Alƙalin Alƙalan Nijeriya da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.
Da take ƙarfafa buƙatarta, ƙungiyar ta ce ya zama dole a yi adalci ga ma’aikata ta hanyar sake duba albashi nan take, tare da ɗaga mafi ƙarancin albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya zuwa N300,000 da kuma sanya N1.5m a matsayin mafi girman albashi ga ma’aikatan mataki na 17.
FWF ta ce, buƙatar ta ta samo asali ne daga abin da ta bayyana a matsayin rashin cikakken aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da aka amince da shi a shekarar 2024.
Kungiyar ta yi zargin cewa har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta aiwatar da cikakken ƙarin albashin da ya kamata ya biyo bayan sabon mafi ƙarancin albashin ba, tare da wasu alawus-alawus da ke da alaƙa da sauyin.
Ta ce, “Abin mamaki ne a ji cewa Gwamnatin Tarayya ba ta kammala aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin ƙasa ba tun watan Yulin 2024. Mun shafe lokaci muna gwagwarmayar ganin an yi cikakken ƙarin albashin da ya kamata ya biyo bayan sauyin.”
A cewar ma’aikatan, sake duba albashin da aka yi a shekarar 2024 ya ɗaga mafi ƙarancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000, amma maimakon a yi ƙarin da ya dace bisa matakan albashi daban-daban, sai aka ƙara wa kowane ma’aikacin gwamnatin tarayya N40,000 kacal.
Kungiyar ta ce tashin farashin kayan abinci, sufuri, haya, wutar lantarki, iskar gas da sauran abubuwan buƙatun yau da kullum ya sanya N70,000 bai wadatar da ma’aikata ba.
Ta ce, ma’aikatan gwamnatin tarayya sun shafe lokaci suna jure wannan hali, amma matsin rayuwa ya kai wani mataki da ba za su iya ci gaba da ɗauka ba.
“Ma’aikatan gwamnatin tarayya suna mutuwa sannu a hankali; muna shan wahala a shiru. Albashinmu ya yi ƙaranci, bai isa ya kai mu gida ba,” inji ƙungiyar.
FWF ta kuma yi zargin cewa wasu ma’aikatan gwamnati sun shiga cikin matsananciyar bashi daga cibiyoyin bayar da ƙananan rance da manhajojin rancen kuɗi na intanet domin samun abin biyan buƙatun yau da kullum.
Ta ce, wasu ma’aikata har suna amfani da manhajojin rancen kuɗi na waya domin samun kuɗin mota zuwa wuraren aikinsu.
Kungiyar ta kuma yi iƙirarin cewa wasu ma’aikata sun koma amfani da itacen girki saboda rashin iya sayen iskar gas.
A cewarta, ci gaba da taɓarɓarewar yanayin kuɗin ma’aikata na iya rage ƙwazonsu a wuraren aiki, tare da samar da yanayin da zai iya ƙara jefa wasu cikin haɗarin cin hanci da rashawa.
FWF ta danganta buƙatarta da ƙarin kuɗaɗen shiga da Gwamnatin Tarayya ke samu da kuma ƙarin kashe-kashen kuɗin gwamnati.
ƙungiyar ta bayyana ma’aikatan gwamnatin tarayya a matsayin “ginshiƙan gudanar da gwamnati”, tana mai cewa ya kamata su amfana da ƙarin kuɗaɗen da ƙasa ke samu.
Ta ce ma’aikatan ne ke samar da damar gudanar da harkokin gwamnati, amma a lokaci guda ana barin su cikin matsanancin hali na rayuwa.
A cikin tsarin albashin da ƙungiyar ta haɗa da wasiƙar, ta nemi a fara da N300,000 ga ma’aikacin mataki na 1, mataki na 1, sannan albashin ya riƙa ƙaruwa a hankali har zuwa N1.5m ga jami’in mataki na 17, mataki na 1.
Tsarin da ta gabatar ya tanadi:
Mataki na 2 — N330,000, Mataki na 3 — N360,000, Mataki na 4 — N390,000, Mataki na 5 — N420,000, Mataki na 6 — N450,000, Mataki na 7 — N480,000, Mataki na 8 — N510,000, Mataki na 9 — N550,000, Mataki na 10 — N600,000, Mataki na 12 — N700,000, Mataki na 13 — N750,000, Mataki na 14 — N800,000, Mataki na 15 — N1,000,000, Mataki na 16 — N1,200,000, Mataki na 17 — N1,500,000.
Kungiyar ta ce shawarar N300,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ta dogara ne kan hasashen kuɗin da ma’aikaci ke kashewa a wata wajen abinci, sufuri, haya, kula da iyali, wutar lantarki, iskar gas, waya da intanet, ruwa da sauran buƙatun yau da kullum.
FWF ta ce tana ganin tsarin da ta gabatar ya dace da halin da ake ciki, kuma gwamnati za ta iya ɗaukar nauyin sa cikin kasafin kuɗin da ake da shi, la’akari da ƙarin kuɗaɗen shiga da kuma abin da ake samu daga sayar da ɗanyen mai.
