*Rasuwarsa, tarihinsa, iyalinsa da nasarorinsa
*Sarkin Musulmi ya jagoranci yi masa addu’a ta musamman
*Tinubu, gwamnatin Bauchi, JIBWIS da sauran al’umma sun nuna juyayinsu
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Al’ummar Musulmi a Nijeriya da ƙasashe maƙota suna ci gaba da alhinin rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran ɗariƙar Tijjaniya, Sheikh ɗahiru Usman Bauchi bayan shafe shekaru kusan 100 a duniya.
Rahotanni sun bayyana cewa, fitaccen malamin ya rasu ne a daren Laraba, wayewar Alhamis, lamarin da ya kawo ƙarshen jagorancinsa na miliyoyin al’umma a Nijeriya da ma ƙasashen waje.
A ranar 28 ga Yuni, 1927 aka haifi shehin malamin a Garin Nafaɗa da ke da tsohuwar Jihar Bauchi, wanda a yanzu kuma yake yankin Jihar Gombe.
Sarkin Musulmi ya jagoranci yi masa addu’a ta musamman:
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya jagoranci addu’a ta musamman ga fitaccen malamin addini, Sheikh ɗahiru Usman Bauchi.
Mai Alfarmar ya jagoranci wannan addu’a ne a yayin da ya halarci wani bikin saukar Alƙur’ani na yara 432 da aka gudanar a garin ƙaura Namoda.
An haifi sheikh ɗahiru Usman Bauchi a ranar 29 ga Yunin 1927 (2 Muharram 1346 AH) a Nafaɗa (wadda a lokacin ke ƙarƙashin jihar Bauchi, amma a yanzu tana ƙarƙashin jihar Gombe).
Sheik ɗahiru ya haddace Alƙur’ani tun yana ƙarami har zuwa matakin hafizi. Sannan ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da fannonin ilimin tafsiri, tasawwuf da fikihu.
Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban giɓi – Tinubu:
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaɗuwa da rasuwar jagoran Tijjaniyyar, Sheikh ɗahiru Usman Bauchi.
A cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana Sheikh ɗahiru Bauchi a matsayin jagoran da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa, wa’azi da jagorantar al’ummar Musulmi.
Tinubu ya ce rasuwar malamin ba wai asara ce ga iyalansa da almajiransa kawai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.
“Sheikh ɗahiru Bauchi malami ne, uba ne kuma murya ce ta daidaito da hikima. A matsayinsa na mai wa’azi kuma babban mai fassarar Alƙur’ani mai tsarki, ya kasance mai kira ga zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban givi,” inji Shugaban ƙasa.
Ya tuna da albarka da ya samu daga marigayin a lokacin shirye-shiryen zaven 2023.
Shugaban ƙasa ya miƙa ta’aziyya ga almajiran malamin a faɗin Nijeriya da wajen ƙasar, yana mai kira da su dawwamar da sunansa ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, tsoron Allah da kyautatawa ɗan adam.
Gwamna Bala, gwamnatin Kano, JIBWIS da Kwankwaso sun yi ta’aziyyarsa:
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar fitaccen malamin a matsayin babban rashi ga al’umma bakiɗaya. Gwamna Bala ya bayyana malamin a matsayin jagoran haɗin kai, zaman lafiya, da fahimtar juna tsakanin Musulmi da mabiya addinai daban-daban.
A cikin saƙon ta’aziyya da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, gwamnan ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi tana alhinin rasuwar malamin. Gwamnan, ya ce Sheikh Dahiru Bauchi babban malami ne na addinin Musulunci, mai imani, tawali’u da hikima. A cewarsa ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa addinin Musulunci, koyar da Alƙur’ani, da kuma taimaka wa mutane wajen tarbiyya.
Marigayin, ya koyar da dubban ɗalibai da suka haddace Alƙur’ani tare da yaɗa addinin Musulunci a sassan nahiyar Afrika. Gwamnan, ya ƙara da cewa gudunmawar da marigayin ya bayar a fannin tafsiri, fiƙhu da tarihi sun taka muhimmiyar rawa wajen ɗora al’umma kan turbar tsira.
Har ila yau, ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi za ta ci gaba da girmama marigayin ta hanyar tallafa wa makarantu da manufofin da ya gina, musamman a fannin ilimin addinin Musulunci, tarbiyya da ci gaban al’umma. Ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya sanya shi a Aljannatul Firdausi, ya kuma bai wa iyalansa, mabiyansa da ɗaukacin al’ummar Musulmi haƙurin rashinsa.
Ita ma Gwamnatin Kano ta miƙa ta’ziyyar rasuwar malamin cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ibrahim Waiya ya fitar. A madadin ƙungiyar Izala (JIBWIS), Shugaba Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau ya bayyana ta’aziyya ga iyalan Sheikh ɗahiru Usman Bauchi da al’ummar jihar Bauchi da Nijeriya baki ɗaya, bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci.
A cikin jawabin ta’aziyya, da aka wallafa a shafin ƙungiyar na Facebook, Sheikh Dr. Bala Lau ya roƙi Allah Ya gafarta wa Sheikh ɗahiru Bauchi duk kura-kuransa, Ya ba iyalansa da danginsa haƙuri da juriya.
Haka nan Shugaban ƙungiyar Izala (JIBWIS) na ƙasa, Sheikh Bala Lau, ya bayyana cewa, rasuwar Sheikh ɗahiru Bauchi babban rashi ne ga addinin Musulunci da al’umma baki ɗaya tare da jaddada cewa, Allah Ya sa Aljanna ta kasance makoma gare shi.
Kazalika shi ma tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana matuƙar baƙin ciki kan rasuwar Sheikh ɗahiru Usman Bauchi, inda ya ce labarin ya kasance babban rashi ga Nijeriya da Musulmai baki ɗaya. A cikin saƙon ta’aziyya da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya ce ya samu labarin rasuwar malamin “da matuƙar baƙin ciki, amma tare da cikakken miƙa wuya ga nufin Allah.”
Ya yaba wa Sheikh ɗahiru Bauchi a matsayin jagora na ilimin addinin Musulunci wanda koyarwarsa ta tarbiyyantar da al’umma ta hanyar cibiyoyin iliminsa da kuma zaman Tafsirin da miliyoyi ke halarta a faɗin ƙasar. Kwankwaso ya jaddada irin matsayin malamin a matsayin shugaba nagari, mai kawo zaman lafiya da haɗa kan jama’a, inda ya ce shugabancinsa na ɗabi’a da biyayya ga Alƙur’ani da Sunnah sun bar babban tasiri a rayuwar al’umma da tarihi. Tsohon gwamnan ya miƙa ta’aziyya a madadin iyalinsa da abokan aikinsa ga iyalan malamin, ɗalibansa, da gwamnati da mutanen Jihar Bauchi. Ya roƙi Allah Ya jiƙan mamacin, Ya gafarta masa kurakuransa, kuma Ya saka shi Aljannah Firdaus. Ameen.
Ayyukansa da gudummawarsa:
Sheikh ɗahiru ya fara gabatar da tafsirin Alƙur’ani a bainar jama’a tun a shekarar 1948 kamar yadda majiyoyi da dama suka nuna, kuma a hankali ya zama ɗaya daga cikin fitattun masu tafsirin Alƙur’ani a nahiyar Afirka ta Yamma.
Daga shekarar 1970s, aka fara saka karatun tafsiransa a gidajen rediyo — rediyon Bauchi (1976), Radiyon Kaduna (1980) da ma sauran gidajen rediyo a Arewa, musamman a watan azumin Ramadan.
Haka kuma ya kafa makarantu da dama na allo da cibiyoyin koyar da karatun Alƙur’ani. Yakan dauki ɗalibai ya ba su masauki da abinci ba tare da sun biya kuɗi.
Ta hanyar gidauniyarsa ta Dahiru Bauchi Foundation, yana tallafawa karatun allo har ma da na boko domin rage matsalolin da almajirai ke fuskanta.
Game da iyalansa:
Sheik ɗahiru yana da iyali mai girma, inda rahotanni suka nuna yana da kimanin ’ya’ya 100 da jikoki sama da 400.
Yawancin ‘ya’yansa da jikokinsa mahaddata Alƙur’ani ne a matsayin gadon gidansu.
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kafa tarihin zama mutumin da ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a tarihin duniya.
Alƙaluma sun nuna cewa shehin malamin, wanda a kwanan nan ya cika shekara 100 a duniya, yana da ’ya’ya da jikoki da ma tattava-kunne kusan 300 da suka haddace Alƙur’ani.
A cewar kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, waɗanda suka karrama malamin da lambar yabo, Sheikh ɗahiru Bauchi shi ne mutum na farko da ya tava samun irin wannan baiwar.
Bayanai sun nuna fitaccen malamin yana da ’ya’ya 95 da jikoki 406 da tattava-kunne 100. Daga cikin wannan adadin, ’ya’yansa 77 da jikoki 199 da kuma tattava-kunne 12 ne suka haddace Alƙur’anin.
Sheikh ɗarihu Bauchi ne daga cikin halifofin Shehu Ibrahim Inyass, Halifan ɗarikar Tijjaniyya, bayan wanda ya assasa ta, wato Sheikh Ahmadu Tijjani.
Yana daga cikin manyan malaman Musulunci a Nijeriya, shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar ƙoli da ke bayar da Fatawar Musulunci a Nijeriya sannan babban jigo ne a ɗarikar Tijjaniya a Nijeriya da ma Afirka.
A zantawarsa da ’yan jarida shekarun baya a Bauchi, Sheikh ɗahiru ya ba da takaitaccen tarihinsa, inda ya ce, “Tarihina dai ni Bafulatani ne, dukanin kakannina hudu Fulani ne, domin kowane mutum yana da kakanni hudu — ta wajen mahaifinsa biyu, ta wajen mahaifiyarsa biyu.
“To ni dukanin kakannina Fulani ne babu inda muka haɗu da wata ƙabila ta kowace fuska. Mu Fulanin Bauchi ne a lokacin da Jihar Bauchi take haɗe da Jihar Gombe.
“Bayan da aka raba Jihar Bauchi da Jihar Gombe, sai muka zama mu Fulanin Jihar Bauchi ne, a lokaci guda kuma Fulanin Jihar Gombe ne.
“Ta wajen mahaifina ni Bafulatanin Jihar Bauchi ne, ta wajen mahaifiyata ni Bafulatanin Nafada ne da ke Jihar Gombe.
“An haife ni ne a watan Janairun 1927, wanda ya yi daidai da watan Muharram 1346 Bayan Hijira, a ranar Laraba.”
Ya ce abin da ya fi ba shi sha’awa a rayuwarsa shi ne irin yadda ya mayar da Alkur’ani sana’arsa da kuma yadda ya rungumi Darikar Tijjaniya ta zama rayuwarsa.
“A duk lokacin da nake hutu ina shagaltuwa ne da karatun Alkur’ani da karanta Salatul Fatihi da tasbihi da istigfari da salatin Annabi (SAW) da sauran zikirori,” inji shi.
Da aka tambaye shi kan fannonin ilimin da ya fi ƙwarewa, shehin malamin ya ce, “Na yi dukkan karatuna na addini a ƙarƙashin kulawar mahaifina, har na haddace Alkur’ani kuma ta hannunsa ne na karvi ɗarikar Tijjaniya.
“Shi mahaifina ya karvi ɗarikar Tijjaniya ne ta hannun wani mutum mai suna Alhaji Gwani Abba, daga baya sai mahaifina ya ba ni izinin na tafi duk inda nake so domin zurfafa ilimina na addini da haddar Alƙur’ani mai girma.
“Vangaren da na fi ƙwarewa sosai shi ne Alƙur’ani, daga nan kuma sai vangaren Tafsiri, a nan malaman Tafsiri sun ce lallai na iya tafsiri inji su.
“Sai kuma vangaren Ma’arifa, ma’anar Ma’arifa shi ne ilimin (gyaran) zuciya wanda ake kiran sa Ilimin Tarbiyya.
“A nan ma masu irin ilimin kan ce ina da sani a fannin. Shehu Ibrahim ya ce lallai na san wannan vangare.
“Sauran ilimomi kuma ina tattavawa, su Hadisi da Lugga da Li’irabi da Tasrifi da Fikihu, duk ina tattavawa,” inji shi.
Shehin malamin ya zama masanin Tafsirin Alkur’ani Maigirma wanda ya samu lambobin yabo a wannan vangaren.
Ya kuma samu digirin girmamawa a vangarori daban-daban a Nijeriya da ma ƙasashen waje.
Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa ta ba shi lambar yabo ta Digirin girmamawa, sannan Gwamnatin Tarayya ta ba shi lambar girmamawa ta ƙasa ta OFR.
Nasarorin Sheikh ɗahiru Bauchi:
Ga wasu daga cikin nasarorin da Sheikh ɗahiru Usman Bauchi ya samu a tsawon shekarunsa: Ya musuluntar da dubban mutane.
A duk lokaci bayan lokaci yakan karanta Alkur’ani kuma yana yin saukar Alkur’ani a kwana biyu. Ya ba da lazumin ɗarikar Tijjaniyya wa dubban mutane da dama a faɗin duniya. Ya kafa makarantun haddar Alƙur’ani sama da 1500 a Naijeriya da sassan Afirka. Sama da mutum 140,924 sun haddace Alƙur’ani a makarantunsa a faɗin Nijeriya. ƙarƙashin gidauniyasa, an gina ɗakunan karatu guda 133,060 a Arewacin Nijeriya.
Mutum ne mai kishin ƙasarsa Nijeriya wanda aduk lokacin da ya buɗe baki zai yi addu’a sai ya roƙi Allah Ya ba ƙasar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Bugu da ƙari, malamin yana cikin waɗanda suka fi kowa daɗewa suna tafisirin Alƙur’ani da watan azumin Ramadan.
Masallacin da yake tafsirin da ke unguwar Tudun Wada a Kaduna, na ɗaya daga cikin manyan masallatan da ke cikin garin, kuma za a iya cewa a tsawon shekaru, malamin yakan zauna a garin kusan fiye da a ko’ina.
Wani bincike da wani wanda ya yi nazari kan rayuwar malamin ya kuma rubuta littafi a kansa mai suna Shehu ɗahiru Bauchi Ginin Allah, shekaru uku da suka wuce, Farfesa Khalid Abdullahi Zaria, ya ce ɗaya daga cikin almajiran shehin, Malam Ahmad Tijjani Kolo, ya ce a yanzu an samu ƙarin mahaddata a cikin zuri’arsa, inda yanzu suka doshi 300. Ya ce da wahala a sami mai irin wannan a tarihi.
Shugaban ƙungiyar ɗaliban Sheikh Dahiru Bauchi, Malam Ibrahim Imam Ismaila, ya ce a tarihi babu wanda ya tava samun irin baiwarsa.
