KSTA ta fara gina tashar mota ta dindindin kan Naira biliyan biyu a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Janaral Manajan hukumar sufuri (KSTA) malam Haruna Musa Rigoji ya faɗi haka a lokacin da yake gabatar da sabbin ministocin haya da hukumar ta saya.

Ya ce tuni gwamnatin Katsina ta bai wa hukumar Naira biliyan ɗaya a yayin da hukumar za ta samar da sauran kuɗin aikin ginin.

Rigoji ya bayyana cewa hukumar za ta samar da kuɗin aikin ne ta hanyar kuɗaɗen shiga da take samu.

Ya faɗi cewa yanzu haka aikin gina Tashar ta dindindin tayi nisa kuma da zarar an kammala aikin duk motocin hayar mallakan hukumar za su koma can tare da ma’aikatan hukumar.

Ya gabatarwa gwamna Dikko Raɗɗa da motocin da hukumar ta saya kirar tayota Homa mai ɗaukar fasinja 14 da.

Shugaban hukumar yace ya zuwa yanzu hukumar cikin shekara biyu ta sayi irin waɗannan motoci guda 33.

Ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa kulawar da yake bai wa hukumar.

A nasa jawabin Gwamna Dikko Raɗɗa ya yabawa Janaral Manajan hukumar bisa yadda yake jagorantar hukumar kan gaskiya da riƙon amana.

By ukarofi