Marubuci da ɗan jarida tagwayen juna ne – Zaidu Barmo

“Ƙaunar juna da son zumuncin marubuta ya sa nake son su”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Sunan Zaidu Ibrahim Barmo wanda aka fi sani da Mr Zaid ba baƙo ba ne, musamman a tsakanin marubutan adabi, saboda yadda yake da son zumunci da kishin yaɗa harkokin rubuce rubucen Hausa. Matashi ne ɗan ƙwalisa daga Jihar Katsina wanda ya shafe shekaru yana rubuce rubuce a ɓangarorin rayuwa daban daban, kama daga kan zamantakewa zuwa mu’amala ta yau da gobe. Bayan kasancewar sa ɗan kasuwa, Zaidu ɗan jarida ne da ya buɗe shafin Mujallar Zauren Marubuta, inda ake ba da labarin rayuwar marubuta da cigaban su. Duk da kasancewar sa matashi, wanda bai taɓa aure ba, kishi da nacin bincike ya sa shi yin wasu rubuce rubuce na shawarwari ga ma’aurata, domin gyara wasu kura-kurai da yake gani a zaman auratayya ta Malam Bahaushe. Shafin Adabi na wannan mako ya gana da matashin marubuci Mr Zaid, don jin gudunmawar sa ga harkar adabi.

MANHAJA: Ko za ka gabatar da kanka ga masu karatu?

BARMO: Sunana Zaidu Ibrahim Barmo, matashi, marubuci, ɗan jarida kuma ɗan kasuwa. Ni Bakatsine ne daga ƙaramar Hukumar Jibiya. Ni ne shugaban Shafin Mujallar Zauren Marubuta da ke Facebook.

Ba mu taƙaitaccen tarihin rayuwarka.

An haifeni a ƙauyen Magama, wani yanki na ƙaramar Hukumar Jibiya, amma yanzu Ina zaune ne a cikin birnin Katsina. Na fara karatu a makarantar rainon yara da firamare a Kaga Jibrin Primary School. Na kuma yi karatun sakandire a mabambantan makarantu, ammana gama a makarantar sakandiren gwamnati ta kimiyya dake Magama. Na kuma koyi ilimin sarrafa na’ura mai ƙwaƙwalwa a Hukumar Samar da Ayyukan yi ta NDE, inda na samu shaidar Satifiket, kafin na ci gaba da karatu. Na yi karatun neman ilimin malanta a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Katsina, inda na mayar da hankali kan nazarin harshen Hausa da zamantakewa wato Hausa/Social Studies.

Ina ka samu ƙwarin gwiwar fara rubutu?

Na fara samun sha’awar rubutu ne tun daga daga makarantar firamare. A lokacin akwai wani malaminmu da ke karanta mana littattafan Hausa, irin su ‘Magana Jari Ce’, ‘Ruwan Bagaja’ da sauran su. A ajin mu na fi kowa natsuwa na saurara, don har zuwa nake yi ofishin malamai wato ‘Staff Room’ in kira malamin in lokacin shi ya yi bai zo ba, don kawai yazo4 ya karanta mana littafi. To, bayan an yi wa malamin canjin wajen aiki daga makarantar sai na riƙa samun litattafaina ina rubutun labari, har ma ina haɗawa da zane, irin dai nima ga littafi ina rubutawa. Da haka har na shiga matakin sakandire, inda ya zama min mabuɗi na ci gaba da rubuce rubuce.

Kawo yanzu ka yi littattafai sun kai nawa, kawo bayanin wasu daga cikin su a taƙaice.

Na rubuta litattafai sun kai goma sha biyar, da suka haɗa da na labaran hikaya da na faɗakarwa, wasu daga ciki ma tuni sun ɓace daga wajen aro a karanta. Amma Ina iya tuna ‘Matar Bahaushe’, ‘Baƙuwar Dare’, ‘Mutumin Facebook’, ‘Sadauki Na’im’, ‘Tabarmar Sarki’, ‘Ƙididdiga’ da kuma na faɗakarwa da tarihi da suka haɗa da littafin ‘Tarihin Garin Jibiya’, ‘Shawarwari 100 Ga Ma’aurata’ da kuma ‘Sirruka Na Musamman Ga Maza Da Mata’.

Kamar shi littafin ‘Mutumin Facebook’, labari ne kan samari makwaɗaita da na nuna su yi taka-tsan-tsan kan mutanen da suke mu’amala da su a Facebook, saboda zamani ya canza ba kowa ne yake tare da kai don Allah ba, sannan ba kowa ne za ka ba yarda kai tsaye a lokaci ɗaya ba, saboda ganin dariya a fuskar mutum ba shi ke nuna har cikin zuciyarshi dariyar ce ba.

‘Shawarwari 50 Ga Iyaye Zuwa Ga ‘Ya’yansu’, wasu shawarwari ne da na ba iyaye kan tarbiyyar da ‘ya’yansu da yadda ya kamata su tafi da su. Saboda lokuta da yawa iyaye na sakaci kan ‘ya’yansu tun suna yara, sai abin ya yi tsamari su dawo su rasa daga ina ɓarakar ta fara, shine na kawo shawarwarin daki-daki a matsayin gudunmuwa ga iyaye kan ‘ya’yansu.

Ka buga littattafan ne ko a ‘online’ ka ke fitar da su?

Na buga guda uku, su ne, ‘Tarihin Garin Jibiya’, ‘Shawarwari 100 Ga Ma’aurata’ da kuma ‘Sirrika Na Musamman Ga Maza Da Mata’. Sauran duka a ‘online’ na yi su, inda nake sakewa a Facebook.

Gaya mana abin da ke baka sha’awa a kan harkar rubuce rubucen Hausa da ƙungiyoyin marubuta.

Na farko dai Ina son marubuta saboda suna da zumunci, da ƙaunar juna, sannan in abu ya samu ɗaya za ka ga kowa da kowa na murna an tafi gabaɗaya.

Sannan ƙungiyoyin marubuta na ƙoƙari ta hanyar shirya tarurrukan wayarwa al’umma da kai kan wani abu da ake fatan ya zamo ya kawo gyara ga rayuwar al’umma.

Yaya alaƙar ka ta ke da sauran marubuta da ku ke hulɗa tare?

Alhamdulillahi, Ina tare da duk marubuta lafiya, wasu yayyaina ne wasu iyaye, wasu kuma sa’annina ne wato abokai kenan. Idan mun haɗu muna girmama juna, har a tsaya a yi labarin yaushe gamo a kuma tattauna kan rubutu da rayuwa, sannan a baiwa juna shawarwari.

Wacce ƙungiyar marubuta ka ke, kuma wacce gudunmawa ka ke bayarwa?

Ina cikin ƙungiyar Marubutan Jihar Katsina, (KMK). Ni Mamba ne kawai mai biyayya (dariya). Sannan ni ne PRO na Ƙungiyar Tsintsiya Writers Association.

Ba mu labarin Mujallar Zauren Marubuta.

Mujallar Zauren Marubuta shafi ne da na ƙirƙira a tsakanin shekarar 2016 da 2017. Dalilin buɗe shi kuwa shine, a wancan lokacin na duba babu wani shafi ko mujalla da ta ke rubutu kan marubuta kaɗai alhalin har waɗanda ba su kai marubuta ba suna da shafukansu da za ka je ka ga abubuwan su.

Ni kuma na ga darajar rubutu ta wuce haka, shine na ƙirƙiri Shafin Mujallar Zauren Marubuta a Facebook, saboda muna zamanin da ba kowa ne ke iya ɗaukar rubutu a takarda ya karanta ba. Amma ana samun ƙaruwar masu karatu a waya.

Wannan shi ne maƙasudin buɗe shafin a Facebook, don ya zama nan ne wajen da marubuta za su ga labaransu, idan wani ya buga littafi a nan za ka gani, in wani marubuci ya samu ƙaruwa ko aure duk a nan za ka gani. Sannan muna sada marubuta da makarantansu don su tattauna wato ‘live interview’, don su yi masu tambayoyin da suke son yi masu.

Daga baya sai muka koma kan kowa, ba iya marubuta kaɗai ba, muna tattaunawa da jama’a da dama, musamman waɗanda suka haɗu da wani cigaba ko ƙalubalen rayuwa, daga baya suka zama wani abu. Sannan mun yi taron mujallar sau biyu, duk a Jihar Katsina, a 2020 da 2021 yanzu ma a wannan shekarar 2022 in sha Allahu za mu yi a ƙarshen watan Nuwamba. Yanzu haka muna da mabiya dubu 32 a shafin.

Daga fara fitar wannan mujalla zuwa yanzu, kana ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu?

Gaskiya Alhamdulillahi. Sanadiyyar shafin Mujallar Zauren Marubuta na haɗu da waɗanda ko a mafarki ma ban tava tunanin rayuwa za ta haɗa mu waje ɗaya ba, amma sai ga shi mun haɗu a waje ɗaya mun tattauna, kuma muna girmama juna. Sanadiyyar shafin na samu alkhairai da yawa, Gaskiya ga shi na yi suna a sanadiyyar wannan mujalla, suna irin wanda ake so, ba suna na vacin suna ba.

Shin kai dama ɗan jarida ne ko sha’awa ce ta shigar da kai?

A’a, ni ba ɗan jarida ba ne kamar kai, amma dai Ina da sha’awar harkar rubuce rubuce sosai. To, kuma dama ka san shi aikin jarida yana kafaɗa da kafaɗa da harkar rubutu. Shi ya sa in Allah ya yo ka a marubuci za ka ganka tamkar tun can ɗan jarida ne kai.

Saboda kamanceceniyar ayyukan. Ko aikin jarida marubuci ya samu za ka ga yana aikin kamar dama ya saba a baya, fiye da wanda ba marubuci ba.

Daga baya mun ga Mr Zaid ya tsunduma harkar kasuwanci ta kafafen sadarwa. Mai ya ja ra’ayinka?

Bayan na gama karatuna, sai na ga jiran aiki yanzu kamar jiran gawon shanu ne. Don haka na ga tun da ga kasuwa nan a yanar Gizo da bata buƙatar ko naira biyar in dai wayarka akwai caji akwai kuma Data, sannan Ina da wayewa a kanta, sai kawai na tsunduma, sayar da shaddodi, huluna, takalma, akwatunan lefe da sauran kayan maza, mata da na yara.

Ana samun riba kuwa, kuma ko ana fuskantar ƙalubale?

Alhamdulillahi duk kasuwa na da ƙalubale, amma nasarar da ke cikinta ta yi wa ƙalubalen fintinkau, kamar nisan Katsina ne da Legas. In kana duba nasarar, za ka ga ƙalubalen ma ba abin waiwaya ba ne, dan ka san wannan ba mai ƙarewa ba ne.

Amma akwai ƙalubale kamar ni da nake kasuwar yanar Gizo wani zai saka ni in sa kuɗina in kawo abu, sai na kawo ya bar ni da shi, alhalin abin nan ba daidai da ni ba ne, dole Ina ji ina gani zan sayar da shi ƙasa da kuɗin da na saye, ko don ma kuɗina su dawo.

Har wa yau akwai ƙalubalen bashi, wani kana bin sa kuɗi amma sai ya ƙi baka, mafi yawa ba dan sun rasa kuɗin ba.

Wanne buri ka ke son cimma nan gaba a rayuwarka?

Ina son na buɗe kamfanin sayar da kayan sawa na kaina, wato boutique, domin na riqa sayar da suturu na maza da mata. Saboda na lura kasuwar kayan sawa kasuwa ce ta har abada, ko yaushe mutane na saka tufafi sai dai ace an yo sabo kawai, amma dai ana sawa ɗin.

Sannan in ɗauki matasa aiki a kamfanin, saboda in ka taimaki matashi ɗaya kamar ka taimaki mutane goma ne, wani shi yake ciyar da gidansu da ɗawainiyar karatun ƙanne, ka ga zan zama sanadiyyar gyara rayuwar al’umma da yawa ta dalilina.

Wacce shawara ka ke da ita ga matasa ýan’uwanka?

Su tashi su nemi sana’a. Kar mutum ya bari zuciyarsa ta mutu, ya zauna jiran sai wani ya nemo ya ba shi. Ya tsaya ya koyi wata sana’a da shi ma zai nemo ya bayar. Haka ya kamata matashi ya zama, ba wai zaman majalisa ba aikin yi ba.

Itace tun yana ɗanyen shi ake tanƙwara shi, tun kana da sauran ƙuruciyarka ya kamata ka zage ka nemi aikin yi, saboda da ƙananun shekaru ake tara abin da za a ci a gaba, in ka girma sai dai ka ga wasu na yi ba kai ba.

Wacce karin magana ce ta ke tasiri a rayuwarka?

“Inda Rai Da Rabo!” Ita ce ta yi tasiri a rayuwata. saboda na yi wa wannan karin maganar karatun jarrabawa, ma’ana karatun natsuwa na kuma gano cewa, duk abin da ka ke son zama, duk abin da ka ke son cimmawa, in dai ka yi haƙuri ka jajirce ka haɗa da addu’a kuma in da rai to za su zo su wuce kamar ba a yi ba.

To, Masha Allah. Na gode

Ni nake da godiya!