Sin ta sanar da shirin bunƙasa fasahar VR

Daga CMG HAUSA

Ƙasar Sin tana fatan samar da na’urorin da ake kira virtual reality (VR) miliyan 25 nan da shekarar 2026, kamar yadda wani shiri game da bunƙasa fasahar ta VR da aka fitar Talatar nan ya bayyana.

Wani shiri na haɗin gwiwa da ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa da wasu sassa huɗu da abin ya shafa suka fitar tare, ya nuna cewa, darajar masanan’antar VR na ƙasar Sin da suka haɗa da manya da ƙananan na’urori da waɗanda ake sarrafawa, za ta zarce Yuan biliyan 350, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 48.1 nan da shekarar 2026.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa