Kammala aikin tashar ruwa mai zurfi ta Legas zai ingiza bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya

Daga SAMINU HASSAN

A farkon makon nan ne kamfanin gine-gine na CHEC na ƙasar Sin, ya miƙa wa mahukuntan Najeriya aikin ginin tashar ruwa mai zurfi da ya kammala, a yankin Lekki na jihar Lagos dake kudu maso yammcin ƙasar.

Ƙwararru da dama na ganin kammala wannan gagarumin aiki a Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya, zai ingiza ci gaban tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya.

Nasarar kammalar wannan aiki ɗaya ne daga hanyoyin da Najeriya ke morar haɗin gwiwarta da ƙasar Sin, ƙarƙashin shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”.

A matsayinta na mafi girma a Najeriya, kuma daya daga mafiya girma a Afirka, tashar ruwa mai zurfi ta Lekki, za ta bunƙasa hada-hadar shige da ficen hajoji da yawansu zai kai kwantainoni miliyan 1.2 a duk shekara, tare da samarwa ƙasar ƙarin kuɗaɗen shiga ta hanyar haraji da sauransu, kana Najeriyar za ta mori damammakin jawo jarin waje a fannoni daban daban.

Ko shakka babu, wannan tashar ruwa za ta amfani tattalin arziki Najeriya, da ma sauran ƙasashen dake tsakiya da yammacin nahiyar Afirka.

Kazalika tashar za ta samar da guraben ayyukan yi na kai tsaye kusan 200,000, da sauran guraben da ba na kai-tsaye ba.

Wannan muhimmin aiki da makamantasa da ƙasar Sin ke tallafawa wajen samar da kuɗaɗen gudanar da su a Najeriya, da sauran ƙasashen Afirka, na ƙara shaida irin kyawawan manufofin dake ƙunshe cikin manufar Sin, ta tallafawa ci gaban kasashe masu tasowa, da burin ƙasar na bunƙasa haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka a dukkanin fannoni, tare da samar da al’ummar duniya mai makomar bai ɗaya ta fannin ci gaba.