Xi Jinping ya gana da Shugabar Tanzaniya

Daga CMG HAUSA

Da yammacin yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da takwararsa ta ƙasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan a birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar Sin, wadda ta zo ƙasar Sin don ziyarar aiki.

Shugabannin biyu sun sanar da daga matsayin hulɗar dake tsakanin ƙasashensu wato Sin da Tanzaniya zuwa wani babban ƙawancen haɗin gwiwa bisa manyan tsare-tsare.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa