Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Mai girma Sarkin Kasuwar Masarautar Singa, Alhaji Isa Abba Ibrahim, babban ɗan majalisar Sarki a sarakunan kasuwannin Fagge, ya bayyana cewa don tabbatar da sauƙin kayan masarufi ya dawwama da ikon Allah ya sa masarautar Singa ta nemi haɗin kan hukumomin masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci a hukumance da kuma shugabannin kamfanoni masu sarrafa kayayyaki da sauran ƙungiyoyin kasuwannin Kano.
Alhaji Sarki Isa Abba Ibrahim ya bayyana haka ne cikin makon nan yayin zantawa da wakilinmu a Kano.
Haka kuma ya ƙara da cewa, “yanzu haka akwai kasuwar bajekolin kayayyakin buƙatun yau da kullum musamman a wanan lokaci na azumi wanda jama’a da dama sun je kasuwar sun yi cefane cikin sauƙi, wanda hakan ta faru ne sakamakon haɗin kan masarauta ne da sauran masu ruwa da tsaki musaman ma’aikatar ciniki da masana’antu ta Jihar Kano, ƙarƙashin kwamishinanta Alhji Shehu Wada Sagagi da ita kanta Gwamanatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusif wanda tsayawarsa ne da taimakon Allah ne sauƙi daga Allah zai ciga ba da dawwama a kasuwanninmu,” a cewar masarauctar Singa a Kano.
A ƙarshe Sarkin Kasuwar Singa ya yi amfani da wannan dama wajen yin nasiha ga jama’a kan su ji tsoran Allah a dukkanin al’amuransu na yau kullum.
Ya kuma buƙaci al’umma da kowanne mu ya ƙara ƙaimi wajen taimakon marayu da raunana musamman a wanan wata na Ramadan na ƙara ibadu da addu’o’i na neman rahama, ƙaruwar arziƙi da zaman lafiyr Kano da Nijiya.
