Masari ya ƙaddamar da sababbin motocin sufuri mallakar gwamnatin Jihar Katsina

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya ƙaddamar da sabbin motocin sufuri mallakar gwamnatin jihar don inganta harkokin zirga-zirga a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Da yake ƙarin haske yayin duba sabbin motocin, Gwamna Masari ya yaba da ƙoƙarin da hukumar sufuri ta jihar take wajen samar da sabbin motocin ƙirar ‘Hummer’ duk ƙarshen wata.

Haka kuma gwamnan ya yi fatan hukumar za ta cigaba da wannan namijin ƙoƙari wajen ganin an sauƙaƙa harkar sufuri a jihar Katsina.

Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban hukumar sufuri na jihar Katsina Malam Haruna Musa Rugoji, ya ce wannan nasara ta su ta samo asali daga irin gudummawar da Gwamna Aminu Masari ya ke ba su duk lokacin da buƙatar haka ta taso.

Rugoji ya ƙara da cewa wannan ƙaddamar da motoci suna yin sa duk bayan watanni uku ma’ana dai suna sayan mota guda duk wata sai bayan wata uku sai su gabatar.

Babban Manajan hukumar sufurin na jihar Katsina ya cigaba da cewa bisa al’ada duk lokacin da suka sayi motoci suna gabatar wa da gwamnan domin ya gani ya kuma sanya albarka kafin su ɗora su akan hanya domin cigaba da aikin al’umma.

“Daga lokacin da na zo wannan hukuma a matsayin shugaba, mun samu nasarar sayen irin wannan motar qirar Hummer 31 sannan mun sayi motocin gudanarwa da kuma ta ofishin shugaban hukumar,” inji shi.

Daga ƙarshe ya yi fatan ƙara inganta harkar sufuri a jihar Katsina ta hanyar cigaba da sayen motoci duk wata kamar yadda suka saba yi inda ya ce ta haka ne za a iya gamsar da abokan hulɗa.